Wednesday, January 15
Shadow

Duk Labarai

Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira Biliyan 19 wajan kula da jiragen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a cikin watanni 15 da suka gabata

Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira Biliyan 19 wajan kula da jiragen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a cikin watanni 15 da suka gabata

Duk Labarai
An kashe akalla Naira N19.43bn wajan kula da jiragen sama na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a tsakanin watan July 2023 zuwa September 2024. Shafin GovSpend ne dake saka ido kan yanda gwamnati ke kashe kudadenta ya wallafa wadannan bayanai. Hakanan shafin yace a shekarar 2024, gwamnati ta ware Naira N13.55bn dan kula da jiragen na shugaban kasa. Hakan na zuwane dai a yayin da mutane da yawa a Najeriya ke fama da wahala wajan samawa kansu abinci.
Nasan Ana shan wahala kuma ina kokarin kawo gyara amma ba yanzu-yanzu ne Al’amura zasu canja ba>>Shugaba Tinubu

Nasan Ana shan wahala kuma ina kokarin kawo gyara amma ba yanzu-yanzu ne Al’amura zasu canja ba>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa yana sane da ana shan wahala a Najeriya kuma yana kokarin kawo sauyi amma sai an yi hakuri dan ba za'a ga wannan sau yi da gaggawa ba. Shugaban ya bayyana hakane ta bakin sakataren Gwamnatin tarayya, Senator George Akume a wajan taron zagayowar ranar haihuwar Pastor Tunde Bakare inda ya cika shekaru 70 da haihuwa. Shugaban ya kuma bayyana Fasto Tunde Bakare a matsayin gwarzo wanda ya bar tarihi me kyau wanda ba za'a manta dashi ba.
Kalli Bidiyo da hotuna yanda motar Dangote ta buge mutane 3 suka mùtù a Jihar Legas

Kalli Bidiyo da hotuna yanda motar Dangote ta buge mutane 3 suka mùtù a Jihar Legas

Duk Labarai
Hukumar kula da ababen hawa ta jihar Legas, LASTMA ta tabbatar da mutuwar mutane 3 bayan da motar Dangote ta bugesu. Rahoton Daily Post yace motar Dangoten dake tafiya akan titin Ita-Opo, Epe ta samu matsalar birki ne inda hakan yasa ta yi taho mu gama da wasu motocin. https://twitter.com/Lagosreporters_/status/1855938771633533145?t=wGaRJiBP-OFQUcO5-BlCNw&s=19 Shugaban hukumar ta LASTMA, Olalekan Bakare-Oki ya tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakin hukumar Taofiq Adebayo, yace motar ta Dangote ta buge Keke Napep da wata mota dake ajiye a gefe. https://twitter.com/adewaleJMO/status/1855957712321773616?t=fn1mEjTIZyObnJoUM-_CEw&s=19 https://twitter.com/Onsogbu/status/1855973272296591750?t=JNXlLjjnGAXnnLp6mzFP5Q&s=19 Yace direban keke Napep din da...
Ko NLC na iya tilasta wa gwamnoni biyan albashi mafi ƙanƙanta?

Ko NLC na iya tilasta wa gwamnoni biyan albashi mafi ƙanƙanta?

Duk Labarai
Ƙungiyar ƙwadago NLC, ta Najeriya ta umarci ma'aikata a jihohin da gwamnatocinsu ba su aiwatar da sabon tsarin albashi mafi ƙanƙanta ba da su shiryawa tsunduma yajin aiki nan da ranar 1 ga watan Disamba. Ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana cewa jan ƙafar da jahohin ke ci gaba da yi wajen aiwatar da sabon tsarin albashin, wani nau’in cin zarafi da tauye hakki ne. Kungiyar kwadagon ta bayyana umurnin a cikin wata takardar bayan taro da shugabanta, Mista Joe Ajaero ya fitar, lokacin da suka kammala taron majalisar zartarwa ta ƙungiyar a birnin Fatakwal. NLC ta nuna da damuwa da rashin amincewa da jan kafar da wasu jihohin a Najeriya ke ci gaba da yi wajen aiwatar da tsarin albashin mafi karanci na 2024, kuma a cewar ta abu ne da ya saba ma doka, tare da taushe hakkin ma’akata musammam a wan...
Kungiyar IPMAN ta cimma matsaya da Dangote kan sayen fetur

Kungiyar IPMAN ta cimma matsaya da Dangote kan sayen fetur

Duk Labarai
Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya mai zaman kanta IPMAN ta ce mambobinta sun kammala cimma matsaya domin fara siyan tataccen man fetur daga matatar man Dangote kai tsaye. Sun bayyana haka bayan uwar ƙungiyar ta gudanar da taro da mambobinta domin bin bahasin yarjejeniyar da suka cimma da matatar da kuma hanyoyin samun man cikin sauki. Alhaji Zarma Mustapha, wani jigo a ƙungiyar ta IPMAN ya shaidawa BBC shirin da suka yi bayan tattaunawar da suka yi da shugabannin matatar a ranar litinin, inda ya ce wannan mataki da suka ɗauka zai haifar da wadatan man fetur a duk faɗin ƙasar. ''Ina bayar da tabbacin cewa muddin muka fara sayen mai kai-tsaye daga Dangote, ba za a rika samun ƙarancin man fetur a ƙasar nan ba, kuma muna sa ran cewa matatan gwamnati ma za su fara aiki nan bada j...
Atiku Abubakar ƙyashi yake yi wa Shugaba Tinubu – Fadar Shugaban Ƙasa

Atiku Abubakar ƙyashi yake yi wa Shugaba Tinubu – Fadar Shugaban Ƙasa

Duk Labarai
Fadar shugaban Najeriya ta ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar yana ƙyashi tare da baƙin ciki da matsayin Shugaba Bola Tinubu na shugaban ƙasa, muƙamin da ɗantakarar jam'iyyar PDP na muƙamin a 2023, ta ce yake ta faman nema har sau shida amma bai yi nasara ba. Fadar shugaban ta soki Atikun ne saboda shawarar da ya bayar ta sauye-sauyen tattalin arziƙi da matakan yaƙi da cin hanci da rashawa a wani saƙon Tweeter da ya sanya kwanan nan. Wani saƙo da ya fito daga fadar shugaban ƙasar, wanda mai ba shugaban shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ya ce, tun bayan da Atiku ya sha kaye a zaɓen 2023 a hannun Tinubu, ya fi mayar da hankali kan zagon-ƙasa ga Shugaba Bola Tinubu maimakon mayar da hankali kan matsalolin jam'iyyarsa....
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ya ziyarci jihar Sokoto game da Làkùràwà

Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ya ziyarci jihar Sokoto game da Làkùràwà

Duk Labarai
Mai riƙon muƙamin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftana Janar Olufemi Oluyede ya nemi da a haɗakai domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar yankin arewa maso yamma. Janar Oluyede ya yi kiran ne a lokacin da ya kai ziyararsa ta farko a jihar Sokoto a jiya Lahadi, inda ya ziyarci sansanin dakarun da ke Tangaza da Illela. A kwanakin nan ne aka samu ɓullar wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ta addabi yankin jihar Sokoto da Kebbi, wadda ake wa laƙabi da Lakurawa, da aka ce ta fito ne daga yankin Sahel. A ranar Juma'a al'ummar garin Mera da ke ƙaramar hukumar Augie ta jihar Kebbi suka rasa mutum aƙalla 15 a wani artabu da suka yi da mayaƙan ƙungiyar ta Lakurawa. Yayin da ya ziyarci sansanonin Janar Oluyed, ya yaba wa sojojin tare da ba su tabbacin samun cikakken goyo...