
Duka Sanatocin jihar Osun wanda ‘yan PDP ne sun ce Tinubu zasu marawa baya a zaben 2027
Sanatocin jihar Osun sun bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zasu marawa baya a zaben shekarar 2027 duk da yake cewa su 'yan PDP ne.
Sanatocin sune Senator Kamarudeen Lere Oyewumi, PDP, da kuma Senator Olubiyi Fadeyi Ajagunla, sai kuma Senator Francis Adenigba Fadahunsi.
Sun bayyana hakanne a wata sanarwa da suka fitar a babban birnin tarayya Abuja.
Sunce suna goyon bayan shugaba Tinubu ne saboda tsare-tsaren sa sun fara bayar da sakamakon da ake so dan farashin kayan abinci yayi kasa sannan kuma an samu ingancin tsaro.