Sunday, October 11
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: Yanda Akawa shugaban yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, watau Abdulaziz Yari Ihun bama yi a Kaduna

Kalli Bidiyon: Yanda Akawa shugaban yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, watau Abdulaziz Yari Ihun bama yi a Kaduna

Duk Labarai
Wasu Fusatattun Matasa a jihar Kaduna sun yiwa shugaban yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu watau Sanata Abdulaziz Yari ihun Bama yi. An ga Sanatan ya fito daga wani Gida inda ya tarar da dandazon matasa a kofar gidan, sun rika kallon fuskarsa suna fadar bama yi. Duk da akwai 'yansanda da DSS a tare dashi amma basu hana hakan faruwa ba. https://twitter.com/originalproflle/status/2106588477240615337 Sanata Abdulaziz Yari dai ya je Jihar Kaduna gidan Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun inda aka ganshi suna ganawa.
Kalli Bidiyon: Atiku da Amaechi aun tsaya shan Mai a Kaduna inda Atikun yace zan dawo da Tallafin Ma Fetur Insha Allahu

Kalli Bidiyon: Atiku da Amaechi aun tsaya shan Mai a Kaduna inda Atikun yace zan dawo da Tallafin Ma Fetur Insha Allahu

Duk Labarai
' Yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi sun tsaya a wani gidan mai shan mai a Kaduna. Inda jama'a masoya suka taru suna ta cewa Atikun sai kayi. Shima ya fito ya tashi tsaye ya daga hannu inda yace zan dawo da tallafin man fetur Insha Allahu. https://twitter.com/royaltyuso/status/2106446118112375092
Kalli Bidiyon: Yanda wani Bahaushe ke ta shan yabo saboda kudin ajiye da wani mutum ya bashi, bayan mutumin ya rasu ya mayarwa da iyalan mamacin kudin

Kalli Bidiyon: Yanda wani Bahaushe ke ta shan yabo saboda kudin ajiye da wani mutum ya bashi, bayan mutumin ya rasu ya mayarwa da iyalan mamacin kudin

Duk Labarai
Wannan wani Bahaushe ne dake sha yabo sosai a wajan Yarbawa a Lagos. Wani kurma wanda ke da dan tabi akansa ya rika samun kudi yana bashi ajiya akai-akai. Daga baya kurman ya rasu. Koda Bahaushen me suna Idris ya samu labari, sai ya tafi gidan su Idris ya mika musu kudin da ya bashi ahiya. Da yawan yarbawa sun taru suna ta jinjina masa. Saidai daga baya an gano ashe kurman ba rasuwa yayi ba labarin karyane aka rika yadawa https://twitter.com/GossipMillNaija/status/2106308587400167720
Kalli Bidiyon: Yanda wasu sojoji dake daji suka sayi kaza da lemu suke rawa suna wakar Omologo bayan karin Albashin da shugaba Tinubu ya musu

Kalli Bidiyon: Yanda wasu sojoji dake daji suka sayi kaza da lemu suke rawa suna wakar Omologo bayan karin Albashin da shugaba Tinubu ya musu

Duk Labarai
Wannan wasu sojoji ne da aka gani suna rawa suna wakar Omologo a daji a gabansu kuma akwai kaza da lemu. Sojojin na bayyana murnar sune bayan da samun karin Albashin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya musu. A yanzu dai mafi karancin Albashin soja Naira 190,000 ne. https://www.tiktok.com/@user8080727204843byaro/video/7691804573517810965?_r=1&_t=ZN-9AFCtxAbR3O
Kalli Bidiyon: Rev. Ezekiel Dachomo ya je kasar Israyla dan kauwa Benjamin Netanyahu koken abinda akewa Kiristoci a Najeriya

Kalli Bidiyon: Rev. Ezekiel Dachomo ya je kasar Israyla dan kauwa Benjamin Netanyahu koken abinda akewa Kiristoci a Najeriya

Duk Labarai
Fasto daga Jihar Filato, Rev. Ezekiel Dachomo ya tafi kasar Israyla dan kaiwa shugaban kasar, Benjamin Netanyahu koken abinda akewa Kiristoci a Najeriya Ya bayyana cewa zai gayawa Benjamin Netanyahu abinda Kiristocin jihar Filato dama fadin Najeriya ke fuskanta. Dachomo yace kuma yanawa mutanen jihar Filato, Taraba da Benue addu'a. https://twitter.com/masskeemz/status/2106056528696611303
Kamfanin mai na kasa, NNPCL yace yayi ragin Naira 66 akan kowace lita a gidajen mansa dake fadin Najeriya

Kamfanin mai na kasa, NNPCL yace yayi ragin Naira 66 akan kowace lita a gidajen mansa dake fadin Najeriya

Duk Labarai
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya bayyana cewa, yayi ragin farashin man fetur na Naira 66 akan kowace lita a gidajen mansa dake Fadin Najeriya. Kamfanin ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a a shafinsa na X Inda yace yanda za'a samu wannan sauki shine a sauke manhajar sa sannan a yi amfani da ita wajan sayen mai. Sannan ya kara da cewa wannan sauki zai ci gaba da gudana daga ranar 1 ga watan Oktoba zuwa ranar 7 ga watan. Kamfanin yace Tuni mutane suka fara sayen man akan wannan farashin na ragi.
Ya gano wadda zai aura na cin amanarsa da maza har 4

Ya gano wadda zai aura na cin amanarsa da maza har 4

Duk Labarai
Ya taso tun daga Amurka ya je dan auren masoyiyarsa amma sai da jama'a suka taru, ya fiddo Bidiyon shaidar cin amanarsa da take yi da wasu maza har 4 Yace ya samu Bidiyon ne kwanaki kadan kamin ranar daurin auren nasu amma yace ba zai fasa bikin ba. Sai ya tara jama'a zai mata tonon Silili. Jama'a a wajan dai sun tashi suna ta bayar da hakuri https://twitter.com/Kezmag_/status/2105955492946178320