Tuesday, June 30
Shadow

Duk Labarai

Ana bari  Halas dan Kunya: Shiyasa na daina shan Giya>>Inji Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

Ana bari Halas dan Kunya: Shiyasa na daina shan Giya>>Inji Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

Duk Labarai
Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bayyana cewa ya daina shan giyane saboda kunya duk da yasan cewa yasan giyar halas ce. Yace dalilin da yasa yake shan giya shine ya gani a baibul cewa Jesus ya mayar da ruwa giya. Yace dalilin da yasa ya daina sha shine, wata rana ya je yayi wa'azi a sansanin majalisar Dinkin Duniya dake Somalia ya kammala sai ya tafi wani gidan cin abinci dan ya sayi giya. Yace yana shiga sai ya tarar da mutane na ta shan giya amma suna ganinsa sai suka boye giyar, yace sai ya matsa kusa da wani yake tambayarsa me yasa suka boye giyar da suke sha? Sai yace ai shi malam ne basa son yaga suna shan giya. Yace daga nan yawa kansa fada yace duk da giyar ba halas bace amma ya daina sha.
Kalli Bidiyon: Yanda Solar Panels da yawa da aka saka a fadar shugaban kasa, an ma dauke janaretan dake fadar saboda yanzu ga Solar

Kalli Bidiyon: Yanda Solar Panels da yawa da aka saka a fadar shugaban kasa, an ma dauke janaretan dake fadar saboda yanzu ga Solar

Duk Labarai
An ga Solar Panels da aka saka a fadar shugaban kasa dake bayar da wutar lantarki ta hasken rana. A Bidiyon an ji wanda suka dauki Bidiyon na cewa, an ma dauke janaretan dake fadar saboda yanzu an saka solar. Shugaba Tinubu dai yace kada a sake zabensa karo na biyu idan bai samar da wutar Lantarki ba. https://twitter.com/i/status/2049132012875722817
Kalli Bidiyon: Ban ce ‘yan Najeriya basu iya Turanci ba, an min muguwar fassara ne, Inji Shugaban Kenya

Kalli Bidiyon: Ban ce ‘yan Najeriya basu iya Turanci ba, an min muguwar fassara ne, Inji Shugaban Kenya

Duk Labarai
Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya bayyana cewa, an masa fassara ba daidai bane kan maganar da yayi amma shi bice 'yan Najeriya basu iya Turanci ba. Yace yana kwatance ne cewa duk kasashen Afrika sun iya Turanci amma turancin Najeriya wani lokacin sai an fassara maka sannan zaka gane. https://twitter.com/i/status/2049092464393191544
Kalli Bidiyon: Shugaba Tinubu da Kross irin na Kiristoci a wuyansa, Dino Melaye yace shin wai ko shugaban kasan ya raba kafane, mutana Kirista muna Musulunci?

Kalli Bidiyon: Shugaba Tinubu da Kross irin na Kiristoci a wuyansa, Dino Melaye yace shin wai ko shugaban kasan ya raba kafane, mutana Kirista muna Musulunci?

Duk Labarai
A wani Bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta, an ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu an masa wankan tsarki irin na Kiristoci sannan aka rataya masa Kross. Lamarin ya baiwa mutane mamaki kasancewar kowa yasan Tinubu musulmi ne. Dino Melaye na daga cikin wadanda suka bayyana mamakinsu game da lamarin inda yace shin ko shugaban kasar ya raba kafane? https://twitter.com/i/status/2048893423889813783
Bayan da APC suka ji cewa mina shirin barin ADC mu koma jam’iyyar PRP, har sun samar da wani sabon shugaba na bogi a jam’iyyar ta PRP zasu kawo rikici a cikinta>>Inji ADC

Bayan da APC suka ji cewa mina shirin barin ADC mu koma jam’iyyar PRP, har sun samar da wani sabon shugaba na bogi a jam’iyyar ta PRP zasu kawo rikici a cikinta>>Inji ADC

Duk Labarai
Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa, Gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ce gwamnati da aka taba yi wadda sam bata da kunya. Jam'iyyar ta bayyana hakane ta bakin me magana da yawunta, Bolaji Abdullahi. Yace wani abin mamaki shine yanda da jin jita-jita cewa 'yan Adawa na jam'iyyar ADC zasu koma Jam'iyyar PRP, har an samu wasu masu ikirarin shugabancin jam'iyyar PRP sun bayyana. Yace Gwamnatin tarayya da APC zasu ci gaba da karyata cewa, basu da hannu a irin wadannan abubuwan amma Duniya tana ganin abinda ke faruwa.
‘Yan Legas da yawa sun rikice suna cewa ba zasu zabi dan takarar Gwamna Abdulaziz Olajide Jandor ba bayan da ya yi yakin neman zabe da larabci

‘Yan Legas da yawa sun rikice suna cewa ba zasu zabi dan takarar Gwamna Abdulaziz Olajide Jandor ba bayan da ya yi yakin neman zabe da larabci

Duk Labarai
Dan takarar Gwamnan jihar Legas, Abdulaziz Olajide wanda aka fi sani da Jandor ya rubuta Qulillaahumma Maalikal Mulki Tu'til Mulka Man tashaaa'u wa tanzi'ul mulka mimman tashaaa'u, wa tu'izzu man tashaaa'u wa tuzillu man tashaaa'u; biyadikal khayru; innaka 'alaa kulli shai'in Qadeer. Inda yayi yakin neman zabe da ita. Saidai hakan ya jawo cece-kuce sosai inda 'yan Lagos da yawa suka ce saboda me zai rika musu Larabci? Ya musu Yarbanci mana. Da yawa dai sun ce ba zasu zabeshi ba saboda hakan.
Farashin dala a kasuwar Chanji ta yau, Talata

Farashin dala a kasuwar Chanji ta yau, Talata

Duk Labarai
Farashin dala a kasuwar Chanji ta yau Talata, 28 ga watan Afrilu na shekarar 2026 ya fara akan Naira 1,360.19 NGN Farasin dai ya dan sauka zuwa Naira 1,359.23 NGN kamin daga baya ya dawo farashin sama. A kassuwar bayan fage kuwa ta garuruwan Lagos, Kano, da Fatakwal da Abuja, farashin dalar ya farane daga Naira 1,480 NGN zuwa Naira 1,495 NGN akan kowace dala.