Atiku Abubakar ya taya Donald Trump murnar lashe zaben shugaban kasar Amurka
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya taya shugaban kasar Amurka, Donald Trump murnar lashe zaben shugaban kasar.
A sakon da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta, Atiku ya bayyana Tsarin Dimokradiyya a matsayin mafi dacewa duk da yana da matsalolinsa.
Atiku ya kuma bayyana cewa irin gwagwarmayar da Donald Trump ya sha kamin ya zama shugaban kasar darasine babba da ya kamata a lura dashi.
Hakanan Atiku ya kuma taya Donald Trump da mutanen kasar Amurka murnar nasarar zaben inda yace yana fatan Donald Trump din zai taimaka wajan aiwatar da zaben gaskiya a Najeriya da sauran kasashen Duniya.