Saturday, March 14
Shadow

Duk Labarai

Wata Sabuwar cuta da ba’a taba ganin irin ta ba ta kkàshè mutane 50

Wata Sabuwar cuta da ba’a taba ganin irin ta ba ta kkàshè mutane 50

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Congo sun bayyana cewa, wata sabuwar cuta da ba'a santa ba ta kashe mutane akalla 50. Hukumar lafiya ta Duniya, WHO ce ta bayyana hakan inda tace cutar na kuma ci gaba da yaduwa. Mahukunta a kasar na hada kai da hukumar ta WHO dan yin bincike akan wannan sabuwar cuta. Zuwa yanzu, cutar ta kama mutane 431 wanda kuma daga ciki mutane 53 sun mutu. Rahoton yace an fara ganin cutar ne a jikin wasu yara 'yan kasa da shekaru 5 su 3 wadanda suka fara nuna alamun cutar bayan cin mataccen Jemage. Alamomin cutar sun hada da Ciwon kai, Zazzabi, Zawo, da kasala. Kuma yawanci cutar na kisa ne kwana biyu bayan an kamu da ita. Yanayin garuruwan da mutanen ke kamuwa da cutar wanda babu wadatattun asibitoci ne yasa ake samun saurin yaduwar cutar inji WHO.
Ba za’a iya samun zaben gaskiya ba a Najeriya>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan

Ba za’a iya samun zaben gaskiya ba a Najeriya>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, ba za'a iya samun zaben gaskiya ba a Najeriya. Goodluck Jonathan ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka gudanar inda yace babbar matsalar itace akwai masu zabe da ake amfani dasu wadanda babu su a zahiri. Jonathan yace sai an samu shuwagabannin hukumar zabe masu nagarta wadanda da su yi magudi kara su sauka daga mukaminsu kamin a samu abinda ake so. Yace ba hujja bace shugaban hukumar zabe yace wai matsa masa aka yi yayi magudi ba, idan aka matsama sai kace gara ka sauka daka aikata ba daidai ba.
An daure malamai 2 da sukawa dalibansu mata Fyàde

An daure malamai 2 da sukawa dalibansu mata Fyàde

Duk Labarai
Babbar kotun jihar Ekiti ta sanar da hukuncin daurin shekaru 44 ga wasu malamai da aka kama da laifin yiwa dalibansu fyade. Malaman sune Ajibola Gbenga dan shekaru 43 sai kuma Olaofe Ayodele dan shekaru 52. Daya daga cikin yaran da sukawa fyaden me shekaru 17 ta bayyana cewa akwai ranar da daga makaranta ya bata kudi naira 200 yace ta je gaban wani gidan mai ta jirashi. Tace tana tsaye sai ga wata dalibar itama ta je wajan inda tace malamin nasu ne itama yace ta jirashi a wajan Tace suna tsaye sai malamin nasu ya karaso shi da abokinsa ya tafi dasu zuwa wani Otal. Inda anan ne aka kaisu dakuna daban-daban aka yi lalata dasu. Tace daga nan sai malamin ya rika damunta da yawa. Daga nan ta ce sai ta fara sanarwa da mahaifiyarta saboda abin ya dameta. Lauyan yaran ya ...
Akwai matsin tattalin arziki a kasarnan dan haka kada ku tsayawa sana’a ko aiki daya, ku raba kafa dan samun saukin rayuwa>>Shugaba Tinubu

Akwai matsin tattalin arziki a kasarnan dan haka kada ku tsayawa sana’a ko aiki daya, ku raba kafa dan samun saukin rayuwa>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa 'yan Najeriya shawarar cewa su raba kafa, kada su tsayawa sana'a daya. Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na ChannelsTV. Yace ba zai yiyu mutum ya tsayawa sana'a ko aiki daya ba. Yace misali idan akwai gona a kusa da inda kake, sai ka dan yi noma dan samun saukin rayuwa. Ya karkare da cewa ya kamata mutane su samarwa kansu mafita.
Idan da Ngozi Okonjo Iwaela zata fito takarar shugaban kasa, zan zabeta>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad

Idan da Ngozi Okonjo Iwaela zata fito takarar shugaban kasa, zan zabeta>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa, da Tsohuwar ministar kudi, Ngozi Okonjo Iwaela zata tsaya takarar shugaban kasa, zai zabeta. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace sauran wadanda zai zaba daga kasar Inyamurai idan sun tsaya takarar shugaban kasa sun hada da Chris Ngige, Dave Umahi, Ifeanyi Ugwuanyi, Geoffrey Onyeama, da Madam Sharon Ikeazor. Saidai ya sha martani a wajan Inyamurai da yawa inda suka kalubalanceshi da cewa me yasa bai sak...
Dansandan Najeriya ya manto Bìndìgàrsà a gidan giya bayan da yayi mankas

Dansandan Najeriya ya manto Bìndìgàrsà a gidan giya bayan da yayi mankas

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Osun na cewa, Wani Dansanda ya manto Bindigarsa a gidan giya a jihar bayan da yayi Mankas da giya. Rahoton yace lamarin ya farune a Osogbo babban birnin jihar ta osun. An bayyana sunan dansandan da wannan lamari ya faru dashi da sunan Inspector Monday. Saidai yayi karyar cewa ya mayar da Bindigar wajan da suke ajiye makamai, saidai da aka bincika an gano karya yake. Hakan na zuwane yayin da ake tuhumar manyan 'yansandan Najeriya kan batan Bindigu da yawa.
Kai ba karamin yaro bane, ya kamata ka sawa Zuciyarka dangana akan maganar rasa mukamin Minista>>Tinubu ya gayawa El-Rufai

Kai ba karamin yaro bane, ya kamata ka sawa Zuciyarka dangana akan maganar rasa mukamin Minista>>Tinubu ya gayawa El-Rufai

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gayawa tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya hakura da maganar rasa mukamin minista wadda an yi tun tuni. Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga inda yace El-Rufai sai raki yake kamar wani karamin yaro da aka kwacewa biredi. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na ChannelsTV. Onanuga yace kamata yayi El-Rufai ya sakawa ransa dangana ya bar maganar rasa mukamin ministan da yayi. Onanuga yace yana tausayawa El-Rufai dan ya ga Alamar lamarin ya bata masa rai sosai. A jiya ne dai El-Rufai a hirarsa da Arise TV ya bayyana cewa, Tinubu ne ya ki bashi minista ba Majalisa ce ta ki amincewa dashi ba.
Tinubu sai yayi 8 kamin ya sauka, ‘yan Bakin ciki saidai su mutu>>APC

Tinubu sai yayi 8 kamin ya sauka, ‘yan Bakin ciki saidai su mutu>>APC

Duk Labarai
Wani jigo a Jam'iyyar APC me mulki, Tolu Bankole wanda yana cikin kwamitin gudanarwa na Jam'iyyar ya bayyana cewa babu gurbi a Aso Rock sai shekarar 2031 bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kammala wa'adinsa na mulki. Ya bayyana cewa, shugaba Tinubu ba zai sauka daga mulki ba sai ya cika wa'adin da kundin tsarin mulki ya bashi damar yi na shekaru 8. Da yake magana akan hadaka da ake samu tsakanin 'yan adawa da niyyar kayar da gwamnatin Tinubu a shekarar 2027, yace yana baiwa 'yan adawar shawarar dama kada su bata kudadensu da lokutansu. Yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi ayyuka da suka amfani mutane sosai sannan suka habaka tattalin arzikin Najeriya.
Barawo Ya Sace Wayar Wannan Malamain, Bayan Kwana Biyu Kuma Barawon Ya Mutu, Shine Ake Zargin Malamain Da Hannu A Mutuwar Barawon

Barawo Ya Sace Wayar Wannan Malamain, Bayan Kwana Biyu Kuma Barawon Ya Mutu, Shine Ake Zargin Malamain Da Hannu A Mutuwar Barawon

Duk Labarai
BA FADA DA MALAM BA… Barawo Ya Sace Wayar Wannan Malamain, Bayan Kwana Biyu Kuma Barawon Ya Mutu, Shine Ake Zargin Malamain Da Hannu A Mutuwar Barawon Saidai a hirar da aka yi da Malamin ya ce shi ba shida hannu a mutuwar domin hasalima ya yafewa barawon wayarsa da ya sace masa. Malamin ya kuma kara da cewa duk wanda ya ce shine ya kashe barawon wayan nasa, to shima ya jira nasa. Me za ku ce?