Ba’a taba shugaban kwarai mutumin arziki iin Tinubu ba>>Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban da ba'a taba yin irinsa ba wajan jajircewa da yiwa Najeriya aiki.
Ya bayyana hakane jiya kamar yanda jaridar thisday ta bayyana.
Yace shugabanci ba da karfin jiki ake yinsa ba, da kaifin tunani ake yinsa dan haka a daina alakanta lafiyar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da shugabancin da yake.
Ya kuma yi Allah wadai da wadanda suka rika yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dariya a ranar Dimokradiyya data gabata.