Bidiyo: Yanda Dogarin Shugaban kasa ya yanke jiki ya fadi a bainar jama’a
Dogarin shugaban kasar Ghana, Colonel Isaac Amponsah ya yanke jiki ya fadi a yayin da shugaban kasar kewa majalisar kasar jawabi.
Lamarin ya farune ranar January 3, 2025 inda nan da nan mutane suka kaiwa dogarin dauki, bayan bashi kulawar gaggawa, an kuma garzaya dashi zuwa Asibiti.
Shugaban kasar Ghanan, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya dakatar da jawabin nasa inda ya juya dan tabbatar da hadimin nasa ya samu kulawa, kamin daga baya ya juya ya ci gaba da yin jawabin.