Saboda na ki komawa jam’iyyar APC sai kala min shari kala-kala ake>>Inji Gwamnan Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bayyana cewa, Saboda yaki yadda ya koma jam'iyyar APC sai kala masa sharri ake.
Yace ana masa sharrin wai yana da hannu a matsalar tsaron dake faruwa inda yace amma abin jin dadi shine a jihar Bauchi basu fama da matsalar tsaro.
Sannan yayi zargin ana amfani da hukumar EFCC dan a bata masa suna.








