Tuesday, January 14
Shadow

Kiwon Lafiya

Ya ake gane mace ta gamsu

Jima'i
Gane gamsuwar mace yayin jima'i ko, ya ake gane mace tayi releasing ko kuma muce ya ake gane mace ta kawo abu ne dake tattare da sarkakkiya, watau abune me wahala. Hanya mafi sauki itace ka tambayeta shin ta kawo? Wata zata gaya maka gaskiya a yayin da wata karya zata maka, wata kuma ba zama ta iya gaya maka ba. Namiji na jin dadi a ransa Idan ya fahimci cewa yasa mace ta yi releasing ko ta kawo, hakan yakan sa yaji cewa eh lallai shi ya cika jarumi, sannana shima sanin kawowar mace, yana taimakawa wasu mazan kawowa. Irin yanda mata ke releasing ba kala data bane, ya banbanta daga mace zuwa mace. Amma hanyoyi da aka fi game cewa mace ta kawo sune kamar haka: Wata Idan ta kawo zata rirrikeka, Saboda dadi da rikicewa. Wata Idan ta kawo zata tura kanta baya ta rufe idanu Sab...

Ya ake gane mace ta balaga

Gaban mace, Ilimi, Jinin Al'ada, Kiwon Lafiya
Ana gane mace ta balagane ta hanyar canje-canjen dake faruwa a jikinta. Yawanci mata suna balaga ne a tsakanin shekaru 9 zuwa 13, Inda suke Riga maza balaga da shekaru 2. Ga alamun dake nuna mace ta balaga kamar haka: Girman nonuwa: Nonuwan yarinya zasu fara girma suna kara fitowa wake suna girma. Zafin Nono: Saboda girman da suke yi, nonuwan yarinyar zasu Dan rika mata zafi ko kaikai. Warin Jiki: Saboda zuwan balaga, yarinya zata iya fara warin jiki. Fitar Gashi a Hamata da Gaba: Gashin hamatarta Dana gabanta zasu fara fita suna kara kauri suna murdewa. Fara Jinin Al'ada: Yarinya zata iya fara jinin Al'ada. Majinar Farji: Gaban yarinyar zai fara fitar da ruwa me yauki. Kurajen Fuska: Yarinyar zata iya yin kurajen fuska Saboda canjawar da jikinta take. Zata i...

Abubuwan dake kawo ciwon mara

Matsalolin Mara
Abubuwa da yawa na kawo ciwon Mara. Masana ilimin kiwon lafiya sun bayyana cewa yawancin ciwon Mara yana samo asaline daga abubuwan cikin jikin mutum dake daidai mararsa. Ga jadawalin Abubuwan dake kawo ciwon Mara kamar haka: Kananan Hanji. Mafitsara Babban Hanji. Appendix. Ovaries ko ace ma'ajiyar kwayayen haihuwa na mata. Mahaifa. Mafitsara. Bladder ko ace majiyar fitsari. Sannan akwai wani abu da ake cewa Peritoneum Wanda ke baibaye da kayan cikin mutum yake taimaka musu wajan yin aiki yanda ya kamata. Duka wadannan abubuwa idan suna ciwo, mutum zai iya jin ciwon a mararsa. Hakanan koda Idan tana ciwo, zata iya harbawa Mara, suma golaye ko 'yayan maraina idan suna ciwo, zasu iya harbawa Mara. Hakanan infection da gyambon ciki Wanda make kira da u...

Abubuwan dake kara ruwan jiki

Abinci, Kiwon Lafiya
Abubuwan dake kara ruwan jiki suna da yawa, a wannana rubutu zamu bayyana wasu daga cikinsu. Shan Ruwa: Shan ruwa ce babbar hanyar samarwa da jikin mutum ruwa, masana na asibitin The Mayo Clinic na kasar Amurka sun bayar da shawarar cewa, namiji kamata yayi ya rika shan ruwa a kalla Kofi 15.5 watau Kofi goma sha biyar da rabi a kullun. A yayin da ita kuma mace kamata yayi ta rika shan Kofi 11.5 watau Kofi goma sha daya da rabi kullun Dan samun isashshen ruwa a jiki. A shawarce ana son mutum ya rika shan ruwa a duk sanda ya ci abinci ko yaci wani Abu irin su masara, Gyada, kuli, cincin, cake da sauransu. Ana kuma son mutum ya rika shan ruwa tun kamin ya ji kishirwa. Hakanan mutum ya sha ruwa a yayin da yake aikin office, ko gudu ko tafiya me nisa ko motsa jiki, ko tukin mo...

Yadda ake gane sha’awar namiji ta tashi

Jima'i
Sha'awar Namiji na da saukin ganewa, saboda abu kadanne yake tayar da sha'awar yawancin maza. Wani gashin mace zai gani ya tayar masa da sha'awa, wani lalle zai gani, wani kafar mace ko hannunta zai gani ya tayar masa da sha'awa, kai wani ma fuskarta kawai ko lebenta zai gani sha'awarsa ta tashi. Wani kuma da ya ga shacin nonon mace shikenan sha'awarsa ta tashi. Hanya mafi sauki ta gane sha'awar namiji ta tashi itace za'a ga azzakarinsa ya mike. Wani kuma idanunsa zasu yi ja, muryarsa zata kankance.

Alamomin namiji mazinaci

Jima'i
Namiji Mazinaci ba'a ganeshi a fuska amma akwai alamun da zai nuna miki wanda zaki san cewa lallai ba soyayyar gaskiya ce yake miki ba. Wadannan Alamomi sun hada da: Zai rika son ya taba jikinki a koda yaushe. Zai rika son ya rika miki maganar batsa a ko da yaushe. Zai nemi yayi zina dake. Idan zai baki abu, ba zai baki haka siddan ba sai ya nemi yin lalata dake. Zai rika nuna miki hotuna da Bidiyon batsa. Ba zai damu da damuwarki ba, kawai dai abinda ke gabanshi shine ya kwanta dake. Zai gindaya miki sharadin idan zai baki yadda yayi zina dake ba zaku rabu. Zai miki alkawuran abubuwan ban mamaki idan kika yadda ya yi zina dake. A mafi yawan lokuta idan Namiji ya nuna irin wannan halayya to zaki iya gane cewa mazinaci ne ba sonki yake tsakani da Allah ba. D...

Sha awar mace da namiji

Jima'i
Kowane tsakanin namiji da mace suna da sha'awa, saidai bisa al'ada akan ce sha'awar mace ta fi karfi amma ita kuyace ke hanata nunawa. Bincike dai ya tabbatar da cewa, maza sun fi mata tunani akan jima'i,kuma sun fi mata neman yin jima'i, kuma sha'awarsu tafi sauri da saukin tashi fiye da ta mata. A yayin da su kuma mata yanayin sha'awarsu abune me cike da rikitarwa. Malami a jami'ar Indiana ta kasar Amurka, Justin Garcia, PhD, da kuma kwararriya me bayar da shawara kan rayuwar aure, Sarah Hunter Murray, PhD sun bayyana cewa, ba lallai a samu sakamako me kyau ba bayan yin binciken wa yafi karfin sha'awa tsakanin namiji da mace ba. Dalilinsu kuwa shine yawanci maza sukan iya bayyana ra'ayinsu akan irin wannan zance amma mata ba kasafai sukan iya fadar abinda ke ransu ba game da ...

Menene maganin wasa da gaba

Jima'i
Wasu Mata da maza, Musamman wadanda basu da aure sukan yi wasa da gabansu dan su gamsar da kansu a duk sanda sha'awarsu ta motsa. Wannan abu da ake yi, yakan iya zama yau da gobe watau har ya zamana ya zamarwa mutum dabi'a mw wahalar dainawa. A daidai lokacin da abin ya zamarwa mutum dabi'a, kuma ya kara hankali, sai ya ga cewa ya kamata ya daina,anan ne sai a fara neman magani. To maganar gaskiya babu wani magani na likita ko na gargajiya da ake sha dan ya hanaka ko ya hanaki yin wasa da gabanka ko gabanki. Dalili kuwa, dabi'a ne ba cuta ba. Ita kuwa dabi'a, mutum ne da kansa yake hana kansa yi, saidai akan iya bayar da shawarwari. Misali idan mutum na son ya daina wasa da gabansa, ya kamata ya kiyaye wadannan abubuwan: Ya daina kallon Fina-finan batsa. Ya daina h...

Maganin kaikayin dubura

Dubura
Akwai maginin likita na kaikayin Dubura sannan akwai dabarun da mutum zai yi a gida dan magance wannan matsala. A wannan rubutu, zamu bayyana dabarun da za'a iya amfani dasu ne a gida dan magance wannan matsala. Hanya ta farko ta magance kaikayin dubura shine a tabbatar ana wanke jiki da kyau idan an kammala yin kashi. Kada a sa sabulu me kanshi ko a shafa mai ko turare a wajan, kada a goge wajan da tsumma me kaushi, a wanke da ruwa kadai ya wadatar. Idan an ji kai kayi, a daure kada a sosa, sosa kaikayin dubura zai iya maka dadi ko ka dan ji saukin abin na dan lokaci amma abinda yafi shine kada a sosa. Idan abin yayi yawa, ana iya yin wana da ruwan dumi dan samun sauki. A gujewa saka kaya masu matse jiki da zasu iya shiga tsakanin mazaunan mutum su makale, hakan zai karawa ...

Meke kawo kaikayin dubura

Dubura
Abubuwan dake kawo kaikayin dubura suna da yawa, ga kadan daga cikinsu kamar haka: A wasu lokutan cutar da ta taba fatar mutum na iya sawa duburarsa ta rika kaikai ko kuma bushewar wajan musamman lokacin san yi zai iya kawo hakan. Hakanan amfani da sabulu me kanshi ko hoda, ko wani kalar man shafawa a dubura ko gogeta da tsimma ko toilet paper duka na iya sawa ta yi kaikai. Infection irin wanda ake dauka daga wajan jima'i, ko kuma irin wanda yake kama gaban mata, wanda ake cewa ciwon sanyi duk na iya sa dubura kaikai. Basir wanda ke sa dubura ta kumbura ko ta rika fitar da jini ko ta rika zafi duk yana kawo kaikayin dubura. Kalar abincin da ake ci irin su cakulan, Tumatir, abinci me yaji, giya, Kofi da sauransu duk suna sanya dubura ta rika kaikai. Yanayin yanda ake tsaft...