Kalli Bidiyon: Kasar Saudiyya ta gayyaci tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad zuwa sakawa Ka’aba Turare
Rahotanni sun bayyana cewa, Kasar Saudiyya ta gayyaci tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad zuwa sakawa dakin Ka'aba Turare.
Malam Bashir Ahmad da kansa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta inda ya bayyana cewa wannan ba karamin karramawa bace a gareshi.
https://twitter.com/i/status/2032832756166635587
Tsohon Ministan sadarwa, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami ya taya Malam Bashir Murna inda yace yana fatan Allah ya karbi wannan abu a matsayin Ibada ya bashi lada.
https://twitter.com/i/status/2032915410522136738








