Thursday, September 17
Shadow
Digital Imam yayi magana kan komawar dansa Kirista

Digital Imam yayi magana kan komawar dansa Kirista

Duk Labarai
A dokar Kundin tsarin Mulkin Najeriya da Dokar majalisar Dinkin Duniya da dokar Allah ta bashi dama yayi addinin da yake so. Lokacin da Allah zai halicceshi bai yi shawara da kai ba, Dan haka ba ruwanka da harkarsa, ba ruwanka da addininshi, duk abinda ya zaba ya shafeshine bai shafeka ba. Yana da kuma 'yancin ya saba maka a Addini, indai kana da 'yancin ka yi addini iri kaza, to shima yana da 'yancin yayi Addini Iri kaza Inji Sheikh Nura Khalid, Digital Imam a sabon karatunsa bayan da dansa yayi ridda ya bar Musulunci zuwa Kiristanci. https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7681949922307984660?_r=1&_t=ZS-99Tf1RNeHsg
Yanda aka kori daya daga cikin masu gadin hukumar ICPC saboda ya shigar da matar tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai wajan da ake tsare dashi ta ganshi a Asirce

Yanda aka kori daya daga cikin masu gadin hukumar ICPC saboda ya shigar da matar tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai wajan da ake tsare dashi ta ganshi a Asirce

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar ICPC ta kori daya daga cikin masu gadinta me suna Daniel Stephen bayan da ya shigar da matar tsohon gwamnan Kaduna, Aichatou Asabe El-Rufai wajan da ake tsare dashi a asirce suka gana. Rahotanni yace an ga Daniel a kyamarar CCTV yana budewa Asabe kofar baya ta ma'aikatar inda ta shiga wajan mijinnnata suka yi magana da hausa ta tsawon mintuna 15. Daniel dai da kansa ya rubuta takardar cewa ya amince da aikata laifin da ya sabawa ka'idar aiki kuma daga nan ne aka koreshi daga aiki. Mahukunta sunce ba yaune Daniel ya saba baiwa matar El-Rufai damar shiga wajan a asirce ba saidai dubunsa ce ta cika.
Kalli Bidiyon: Martanin Masallacin Sultan Bello kan zargin da wani yawa Sheikh Ahmad Gumi ya rike masa mata

Kalli Bidiyon: Martanin Masallacin Sultan Bello kan zargin da wani yawa Sheikh Ahmad Gumi ya rike masa mata

Duk Labarai
Hadimin Sheikh Dr. Ahmad Gumi, Malam Nasiru dan Agaji ya mayarwa da mutumin da yace zargi malam da rike masa mata. Nasiru yace matar wannan mutumin itace da kanta ta je gidan malam neman taimako kan abinda mijinta yake mata. Yace kuma sun kai magana kotu dan haka babu abinda zasu ce game da abinda ya faru. Mutumin dai ya fito ya zargi cewa matarsa da ya auro daga kasar Morocco ta shafe watanni 11 a gidan Sheikh Dr. Ahmad Gumi inda ya zargesa da riketa. Mutumin dai ya zargi cewa Sheikh Gumi bashi da wata alaka da matar sun hadune a wani shagon sayar da magani. https://www.tiktok.com/@abumaliktv007/video/7681924688896953608?_r=1&_t=ZS-99TSootuVuO