Saturday, January 4
Shadow

Meke kawo ruwan nono ga budurwa

Nono
Yawancin abinda ke kawo ruwan nono shine haihuwa. Bayan mace ta haihu, ruwan nononta na zuwa sosai. Bayan haihuwa akwai wasu abubuwan na daban da kan iya kawowa budurwa ruwan nono: Yawan tabawa da matsa nonon budurwa yana iya sawa ya kawo ruwa. Shan wani magani da jikin budurwar be yi amanna dashi ba yana iya sata reaction ruwan nononta ya kawo. A wasu lokutan ma haka kawai babu dalili, nonon budurwa zai iya kawo ruwa. Yanda ake tsayar da zubar ruwan nono Zubar nono na raguwa da kanta daga lokaci zuwa lokaci. Amma akwai abubuwan da za'a iyayi dan magance matsalar. A daina matsa nonon. Wasu lokutan ana gwada daure nonon da tsumma me kyau.

Zafin kan nono ga budurwa: Maganin zafin kan nono ga budurwa

Duk Labarai
Saka rigar mama da ta matse ki na iya kawo zafin kan nono, hakanan lokacin jinin Al'ada ma budurwa na iya yin fama da zafin nono. Tana iya yiyuwa ciwo ne ko kuma infection ya kamaki. Yawancin mata dake tsakanin shekaru 15 zuwa 40 na fana da ciwon kan nono. Wata kila tana iya yiyuwa magani ne kika sha ko kuma wani abinci ya miki reaction shiyasa kike jin hakan. Maganin zafin kan nono ga budurwa: Saka Rigar mama data yi daidai da nonoki zai taimaka wajan rage zafin. Zaki iya tanbayar likita ko me kemist ya baki magani. Rage shan chocolate, shayi, da lemunkan kwalba irinsu Fanta da Coke. Kina iya samun tsumma me sanyi ko dumi ki rika dorawa akan nonon. Motsa jiki akai-akai ma na taimakawa. Ki ragewa kanki damuwa da bacin rai. Lokacin da ya kamata ki ga likita ...

Kaikayin nono ga budurwa: Meke kawo kaikayin nono ga budurwa

Kiwon Lafiya
Kaikayin nono ga budurwa na iya zuwa saboda wani abu data ci ko kuma haka kawai, ko saboda jinin al'ada, ko bushewar fatar kan nonon da sauransu. Ga abubuwa 11 dake kawo kaikayin nono ga budurwa: Tana iya yiyuwa wajan yayi bori ne ko wani kurjine ya fito akan nonon. Idan kika yi amfani da sabulun da be karbeki ba ko kuma jikinki baya so, zai iya saka kaikai a jiki hadda ma kan nono. Saka rigar mama wadda ta matse ki na iya sawa kan nonon ki yin kaikai. Idan hakane, ki saka rigar mama wadda bata matseki sosai ba. Tana iya yiyuwa kin yi zufa kika barta ta bushe a jikinki, hakan na iya kawo kaikan kan nono. Lokacin Al'ada nasa kan nonon mace ya rika kaikai. Akwai kuma ciwon kansar mama wanda idan kai kayin yayi yawa ya kamata ki je Asibiti.
Ranar Litinin za mu kammala kwashe alhazai – NAHCON

Ranar Litinin za mu kammala kwashe alhazai – NAHCON

Hajjin Bana
Hukumar Alhazan Najeriya wato NAHCON ta ce a ranar Litinin ne za ta kammala kwashe maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki, a daidai lokacin da hukumomin Saudiyya suka sanar da rufe filin jirgin Sarki Abdul'aziz da ke Jeddah. A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, hukumar ta ce "Jirgin karshe na maniyyata zuwa aikin Hajji na shekarar 2024 zai tashi daga Abuja da sanyin safiyar ranar Litinin, 10 ga watan Yunin 2024, inda zai nufi Madina." Ana dai sa ran cewa jirgin zai ɗauki kimanin alhazai 211 daga Zamfara da Sokoto da Kebbi da Bauchi da Abuja da kuma jNeja, tare da rukunin karshe na jami’an aikin Hajji a cikin jirgin na FlyNas. Hakan ne ya kawo ƙarshen "jigilar alhazai na bana zuwa Saudiyya inda Aero Contractor...
Babbar Sallah: ‘Yan Najeriya na kokawa kan tsadar dabbobi

Babbar Sallah: ‘Yan Najeriya na kokawa kan tsadar dabbobi

Duk Labarai
Babbar Sallah: 'Yan Najeriya na kokawa kan tsadar dabbobi. Yayin da babbar sallah ke ƙara ƙaratowa 'yan Najeriya na kokawa dangane da tsadar dabbobi musamman raguna waɗanda su ne aka fi amfani da su a lokacin layya. Wasu masu sayar da raguna da wakilin BBC a Legas ya tattauna da su sun ce farashin raguna ya ninka sau uku daga yadda aka sani a bara. "Ragon da aka saya a bara naira dubu 100 yanzu ya zama naira dubu 300. Haka shi ma na naira dubu ɗari biyu yanzu ya zama naira ɗari biyar". In ji wani mai sayarwa. Su ma masu sayen dabbobin da dama da aka tattauna da su sun ce bai zama lallai su yi layyar ba duk da dai wasu sun ce "amfani kuɗi shi ne a kashe su ta hanyar da ta dace."
Amurka ta fara janye sojojinta daga jamhuriyar Nijar

Amurka ta fara janye sojojinta daga jamhuriyar Nijar

Duk Labarai
Sojojin Amurka sun fara janyewa daga Nijar kamar yadda tashar talabijin ta ƙasar, Tele Sahel ta rawaito. A wani biki da aka yi a Air Base 101 da ke birnin Yamai, babban hafsan sojojin Nijar, Kanal Maj Mamane Kiaou, ya sanar da cewa, sojojin Amurka 260 daga cikin kiyasin 1,100 da aka kiyasta sun janye daga ƙasar tare da tankunan kayan aiki da dama. Maj Kiaou ya bayar da tabbacin cewa Nijar za ta tabbatar da tsaron jami'an Amurka a lokacin janyewar da ake sa ran kammalawa a tsakiyar watan Satumba. Duk da janyewar, ƙasashen biyu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a ranar 8 ga watan Yuni, inda suka tabbatar da cewa dangantakarsu ba za ta ɓaci ba. Janyewar sojojin ta biyo bayan sanarwar da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta bayar a ranar 16 ga watan Maris, inda ta soke yarjejeniyar da t...
Gwamnatin jihar Plateau ta ɗage dokar hana yawo a Mangu

Gwamnatin jihar Plateau ta ɗage dokar hana yawo a Mangu

Tsaro
Gwamnatin jihar Filtao ta bayar da sanarwar dage dokar hana yawo da ta saka tun a watan Janairun wannan shekara a karamar hukumar mulki ta Mangu da kewaye. Gwamnan jihar Caleb Mutfwang ne ya saka dokar hana fitan har na tsawon awa ashirin da hudu a kowace rana, bayan wani hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a kauyukan Punshit da Sabon-Gari inda suka kashe akalla mutum sha uku tare da jikkata karin wasu baya ga kona gidajen jama’a da dama. Gwamnatin Filaton ta bayyana cewa an saka dokar ne domin a samar da cikakken tsaro da zaman lafiya tsakanin kabilu daban-daban da ke fadin jihar.
Blinken a Masar don inganta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Blinken a Masar don inganta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Duk Labarai
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Masar domin samun goyon bayan yankin ga yarjejeniyar zaman lafiyar Gaza da shugaba Joe Biden ya gabatar kwanan nan. Wannan ziyarar dai ita ce ziyara ta takwas da Blinken ya kai yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan ɓarkewar rikicin Gaza. Blinken zai gana da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi kafin ya tattauna da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a yau Litinin. Masu shiga tsakani a yankin ciki har da Qatar, sun shafe watanni da dama suna ƙoƙarin sasantawa tsakanin Isra'ila da Hamas. Netanyahu ya ci gaba da jajircewa wajen ƙin amincewa da duk wani tsagaita bude wuta har sai an wargaza sojojin Hamas da kuma sako duk waɗanda aka yi garkuwa da su. A karshen makon da ya gabata, sojojin Isra'ila sun kuɓutar da wasu mutane hu...