Monday, January 12
Shadow
Da Duminsa: Hukumar ‘yansandan kasar Ghana sun kama Fastonnan da yace za’a yi tashin Qiyama ranar Kirsimeti amma ba’a yi ba

Da Duminsa: Hukumar ‘yansandan kasar Ghana sun kama Fastonnan da yace za’a yi tashin Qiyama ranar Kirsimeti amma ba’a yi ba

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Ghana sun bayyana cewa, Hukumar 'yansandan kasar sun kama fastonnan me suna Evans Eshun da yace wai za'a yi tashin Qiyama ranar 25 ga watan Disamba, watau ranar Kirsimeti. Hukumar 'yansandan ta ce bata yadda da masu amfani da addini suna tayarwa da mutane hankali ba inda tace tabbas an kama Fasto Evans Noah. Saidai bata bayyana laifukan da ake zarginsa da aikatawa ba. Fasto Evans Noah yace wai an masa wahayin za'a yi tashin Qiyama ranar 25 watan Disamba sannan an bashi Umarnin sassaqa jirgin ruwa irin na Annabi Nuhu saboda wai za'a yi ruwan sama. Saidai daga baya da ranar Kirsimeti ta zo ba'a yi tashin qiyamar ba, ya bayyana cewa shi ranar kawai aka sanar dashi, ba'a sanar dashi shekarar da za'a yi tashin qiyamar ba.
An Salami Anthony Joshua daga Asibiti bayan Khàdàrìn da ya rutsa dashi

An Salami Anthony Joshua daga Asibiti bayan Khàdàrìn da ya rutsa dashi

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Ogun sun tabbatar da cewa, an Sallami Shahararren dan Damben Najeriya, Anthony Joshua daga Asibiti bayan Khàdàrìn motar da ya rutsa dashi wanda har ta kai ga abokansa 2 suka rasa rayukansu. Gwamnatin jihar Ogun ce ta tabbatar da cewa an Salami Anthony Joshua daga Asibitin. Ta sanar da cewa, an sallameshi daga Asibitinne ranar Laraba da yamma.
Da Duminsa: A karin Farko, Hukumar Sojojin Najeriya ta yi martani kan kalaman Sheikh Gumi

Da Duminsa: A karin Farko, Hukumar Sojojin Najeriya ta yi martani kan kalaman Sheikh Gumi

Duk Labarai
Hukumar sojojin Najeriya ta yi martani kan kalaman Sheikh Gumi game da hare-haren da kasar Amurka ta kawo Najeriya. Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya yi Allah wadai da harin da kasar Amurka ta kawo Najeriya inda yace hakan rainine. A yayin da yake magana da manema labarai, me magana da yawun hukumar sojojin Najeriya ya amsa wata tambaya da aka masa cewa mw zasu ce kan Allah wadai da Gumi yayi da kawo harin da Amurka ta yi Najeriya? Yace suna sane da abinda Gumi ke cewa, amma ba hakkinsu bane su dauki mataki akansa. Yace akwai hukumomin da ke da wannan Alhakin kuma yasan cewa, zasu dauki matakin da ya dace. https://twitter.com/AsakyGRN/status/2006390924893401363?t=tLObFx3bcrWl5goXd_Eb9g&s=19
Da Sunana Samuel, Amma Na musulunta na koma Mohammed>>Inji Sanata Ali Ndume

Da Sunana Samuel, Amma Na musulunta na koma Mohammed>>Inji Sanata Ali Ndume

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno yace shi da iyayensa duk musulunta suka yi. Yace ya taso a matsayin Kirista kuma ya je makarantar Kiristoci. Sannan yace a da sunansa Samuel amma aka ce ya je ya shiga Musulunci ya koma Mohammed, sannan yace mahaifiyarsa ma tana cikin matan zumunta amma daga baya duk sun musulunta. Saidai yace a gidansu raba kafa aka yi, wasu suka zama musulmai, was suka zama Kirista ta yanda duk inda ta fadi sha. https://twitter.com/OzorNdiOzor/status/2006458422951379229?t=aEfZBD7hjtLPnTHEV2ENmQ&s=19
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sakawa kasafin kudin 2026 hannu, saidai rashin mataimakin gwamna a wajan ya jawo cece-kuce

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sakawa kasafin kudin 2026 hannu, saidai rashin mataimakin gwamna a wajan ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sakawa kasafin kudin shekarar 2026 hannu a yau, Laraba. Kasafin kudin na Naira Tiriliyan 1.4 ne wanda hakan ya samu halartar manyan jami'an Gwamnatin Kano. Saidai rashin ganin mataimakin Gwamnan jihar a wajan ya jawo cece-kuce. Dama dai wata majiya tace Gwamna Abba shi kadai zai koma APC ba tare da mataimakin gwamnan ba. Hakanan a dazu ne muka ga Abba ya gana da shuwagabannin jam'iyyar APC na jihar Kano.
Peter Obi ya koma jam’iyyar ADC

Peter Obi ya koma jam’iyyar ADC

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben shakerar 2023 a jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya koma jam'iyyar ADC. Peter Obi ya koma ADC ne a wani taron jam'iyyar da aka gudanar a jihar Enugu. Yace ba zasu bayar da damar yin magudin zabe a shekarar 2027 ba. Peter Obi kuma ya koma jam'iyyar ta APC ne tare da wasu jiga-jigai na kusa dashi da suka hada da masu rike da mukaman siyasa. u