Wannan wata mata ce da aka binne a akwatin gawa me kirar Kwalbar koka kola.
Matar dai sunan ta Late Madam Efuwari Ego wadda aka bizne a garin Omeya dake karamar hukumar Ogbia ta jihar Bayelsa.
An binneta ne ranar 22 ga watan Nuwamba.
Fitaccen jarumin finafinan masana'antar Bollywood ta Indiya, Dharmendra wanda ake kira da Dharam ya rasu a birnin Mumbai na Indiya yana da shekara 89 a duniya.
Firaministan India Narendra Modi ya bayyana jajensa ga iyalan mamacin da ƴan ƙasar baki ɗaya, sannan ya bayyana rasuwar jarumin da "ƙarshen zangon jaruman sinima a Indiya."
Dharmendra, wanda ya kasance yana bayyana da "mutum mai sauƙin kai" ya daɗe yana jan zarensa a harkar fim, inda yake nishaɗantar da miliyoyin masoyansa a duniya.
Ya yi fice da sunan Veeru saboda rawar da ya taka a fim ɗin Sholay a shekarar 1975, sannan ya fito a finafinai sama da 300 a gomman shekaru da ya yi a masana'antar.
An haife shi ne a ranar 8 ga watan Disamban shekarar 1935 a ƙauyen Nasrali da ke lardin Punjab Ludhiana. Malaminsa a makaranta n...
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya karɓi katin kasancewa ɗan jamʼiyyar ADC a mazaɓarsa ta Jada da ke jihar Adamawa.
Hakan ya kawo ƙarshen tsawon lokacin da ya ɗauka bai bayyana sauyin sheƙar ba, bayan da ya bar PDP.
Ya sanar da hakan ne a shafinsa na X, inda ya wallafa hotunan sa riƙe da katin sabuwar jami'yyarsa, da gajeren rubutu da ke nuna ya shiga jam'iyyar a hukumance.
A ranar 14 ga watan Yulin 2025 ne cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce ya fita daga PDP ba tare da ɓata lokaci ba.
Atikun ya kuma ce wajibi ne ya raba gari da jam'iyyar a yanzu bisa la'akari da yadda ta sauka daga harsashinta na asali.
Bidiyo sun yadu sosai kan yanda matasa suka rika bin 'yan mata da gudu suna kama musu nonuwa a Ado Bayero Mall dake Kano.
Lamarin ya farune a yayin da wani Mawaki ya je wajan yayi wasa.
Daya daga cikin matasan an jishi yana daukar Bidiyo yana cewa hakan bai kamata ba.
An ga wata matashiya dake shirin tsallaka titi Matasan aun daka mata wawa.
https://twitter.com/pressmanng1/status/1992928590871359649?t=mAI3HGfFDnCYBb3qRHZIMA&s=19
Danna nan dan Kallon Bidiyon
https://www.tiktok.com/@umarkabeer03/video/7576024262100749575?_t=ZS-91fKryqbcuG&_r=1
Matar Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin, Maryam ta bayyana cewa, Tun bashi da komai ta aureshi.
Ta bayyana cewa haka ta zauna dashi har ya samu budi ya koma Abuja da zama.
Ta kara da cewa kuma kamin ta aureshi har ce mata aka yi Zarmalulunsa baya aiki amma haka ta rufe ido ta aureshi amma yanzu ya wulakantata.
Ta yi gargadin cewa, a wannan fadan da suke duk wanda ya kara kafeta yana cewa laifinta ne ko ita ce me laifi saita ci Kutumar Bura Ubansa.
https://www.tiktok.com/@amanaatamama2/video/7576069185340460300?_t=ZS-91fG76B7bjF&_r=1
Tauraruwar Tiktok, Sadiya Haruna ta wallafa Bidiyo inda ta saka wakar Ko yau Kasuwa ta watse.
Sannan ta bayyana cewa zawarci ba dadi domin ita shaida ce
Da aka Mata maganar ta raba auren Gfresh da matarsa Maryam kuwa, fashewa ta yi da dariya.
https://www.tiktok.com/@sayyada_sadiya_haruna/video/7576216580007169336?_t=ZS-91fDCXuxWMr&_r=1
Wani me shagon sayar da kayan sawa ya nuna bacin ransa sosai bayan da sabuwar ma'aikaciyar da ya dauka aiki ta samu kyautar Naira Dubu 60 daga wani da ya je shagon.
Yace satin ta biyu kacal da fara aiki a shagon kuma Albashin Naira dubu 50 yake biyanta.
A Bidiyon an ji kuma yana cewa, wani ma ya fara sai mata abinci.
Lamarin dai ya jawi muhawara kan aiki da irin wadannan abubuwan dakan dauke hankalin ma'aikata.
https://twitter.com/CryptoEth1969/status/1992477832266875379?t=00nf-McXsQxQX-B7ac379w&s=19
'
Yansandan Najeriya 5 ne suka rigamu gidan gaskiya bayan Harin Kwantan Bauna da aka Afka musu a jihar Bauchi.
Lamarin ya farune a kauyen Sabon-Sara dake karamar hukumar Darazo ta jihar inda aka kira 'yansanda dan su kawo dauko kan rikicin makiyaya da manoma.
Saidai bayan isarsu wajan wasu 'yan Bìndìgà sun Afka musu da hari inda aka Khashye 'yan Bìndìgàr da yawa.
Daidai 'yansanda 5 ma sun rasa rayukansu.
Wadanda suka rasa rayukan nasu sune :
DSP Ahmad Muhammad (SID)
ASP Mustapha Muhammad (10 PMF)
Inspector Amarhel Yunusa (10 PMF)
Inspector Idris Ahmed (10 PMF)
Corporal Isah Muazu (AKU)
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin a janye jami'an 'yansanda dake baiwa manyan mutane tsaro a fadin Najeriya.
Shugaban yace duk wani babban mutum dake neman jami'an tsaro a bashi jami'an Civil Defence.
Shugaban ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda jami'an 'yansandan dake a ofisoshin 'yansanda dake Fadin Najeriya sun yi kadan.
Hakanan yace duk 'yansandan za'a mayar dasu wajan aikin da shine dama ya kamata suna yi.
Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar bayan taron da shugaba Tinubu yayi da shuwagabannin jami'an tsaro na kasa ranar Lahadi.
Sannan yace shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a dauki sabbin jami'an 'yansanda guda dubu 30.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa sabuwar dokar Haraji ta tanadi tsarin da zai nunawa Gwamnati yanda mutum ke kashe kudinsa.
Ta wannan hayar ne Gwamnatin zata san ainahin yawan kudin shigar mutum.
Shugaban kwamitin shugaban kasa akan Haraji, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi dashi.
Yace za'a bukaci mutum ya bayyana nawa yake samu kudin shiga a Shekara, amma idan mutum yayi Qarya, zasu gani ta hanyar yawan kudaden da yake kashewa.
Yace ta nan ne zasu fahimta kuma su nemi mutum ya biya kudin Haraji, yace idan mutum ki biya, zasu iya diba daga cikin asusun ajiyarsa na banki ba tare da an yi wani rikici dashi ba.
https://twitter.com/OneJoblessBoy/status/1992540377228927482?t=HrKNFcUoyNAIFmu9J155Sw&s=19