Wednesday, March 25
Shadow
EFCC sun kulle gidaje da kasuwancin Tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami

EFCC sun kulle gidaje da kasuwancin Tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami

Duk Labarai
A ranar Litinin, EFCC sun kulle gidaje da kasuwancin tsohon Ministan shari'a Abubakar Malami. Rahotanni sun bayyana cewa EFCC sun rubuta da jan fenti cewa an kulle gidajen kada wanda ya shiga. A wani Bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta, An ga Malami yana tambayar EFCC din ina umarnin kotu da yace a kulle masa gida? Malami dai yace umarnin farko da kotu ta bayar ya dina aiki. Saidai jami'an EFCC din sun bashi amsar cewa zasu iya kulle gidajen nasa tunda har yanzu ana kan binciken su. https://twitter.com/i/status/2036138556024906020
Bani bace, Ni Bazan Mvtv ba, inji matar tsohon Gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai bayan da wani rahoto yace ta rigamu gidan gaskiya

Bani bace, Ni Bazan Mvtv ba, inji matar tsohon Gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai bayan da wani rahoto yace ta rigamu gidan gaskiya

Duk Labarai
Matar tsohon gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ta musanta wani rahoto dake cewa ta rigamu gidan gaskiya. Tace ba ita bace, ita ba zata mvtv ba inda tace ita Allah zai barta. Ta rubuta hakane a shafinta na X. https://twitter.com/i/status/2036050333705588786 Hon. Bello El-Rufai dai ya wallafa cewa matar dan uwan mahaifinsu ta rasu. Inda daga nan ne masu rahoton suka samu matashiyar labarin suka wallafa ba tare da bincike ba.
Rahotanni sun ce Dangote na shirin daina sayar da mansa a Najeriya ya rika sayar dashi duka zuwa kasashen waje

Rahotanni sun ce Dangote na shirin daina sayar da mansa a Najeriya ya rika sayar dashi duka zuwa kasashen waje

Duk Labarai
Wasu Rahotanni sun bayyana cewa, Aliko Dangote na shirin fara sayar da duka man da ya tace a matatarsa zuwa kasashen waje. Rahoton yace Dangote na fushi ne da Gwamnatin Najeriya saboda har yanzu tana baiwa 'yan kasuwa lasisin shigowa da man fetur duk da yake cewa ga matatar mansa tana samar da man. Kasashen Afrika irin su Afrika ta Kudu da sauransu na yiwa Dangote matsin lamba kan ya kara yawan man fetur din da yake sayar musu.
Karya ake min ban taba yin sana’ar Sayar da katin waya ba>>Inji Tsohon Hadimin Buhari, Malam Bashir Ahmad

Karya ake min ban taba yin sana’ar Sayar da katin waya ba>>Inji Tsohon Hadimin Buhari, Malam Bashir Ahmad

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya mayar da raddi bayan da wani yace a da kamin ya shiga harkar siyasa yna sana'ar sayar da katin waya ne. Malam Bashir Ahmad ya bayar da tallafin Naira Miliyan 5 ne a wani shiri da ake yi na tara kudaden da za'a tallafawa matasa da sana'o'i a Arewa. Sai wani yace a da fa sana'ar sayar da katin waya yake. Saida malam Bashir Ahmad ya karyata wannan ikirari. Yace idan da yayi sana'ar sayar da katin waya ba zai ji kunyar fadar hakan ba da itama sana'a ce kuma wasu sun yi sun samu nasara a rayuwa. https://twitter.com/i/status/2036159753030701268
Tinubu na shirin zarcewa a karo na 3 a 2031>>Inji VeryDarkman

Tinubu na shirin zarcewa a karo na 3 a 2031>>Inji VeryDarkman

Duk Labarai
Tauraron dan fafutuka na kafafen sada zumunta, Verydarkman ya zargi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da shirin zarcewa a matsayin shugaban kasa a karo na 3. Verydarkman yace shirin da shugaba Tinubu yake yi bana 2027 bane, yace ya mayar da Najeriya kasar Jam'iyya daya sannan kuma kayan abincin da suke rabawa. Yace wannan shirin zarcewa ne a karo na 3 ba wai na biyu ba. A baya dai, Me yunkurin kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho ya bayyana cewa, zasu tabbatar shugaba Tinubu ya zarce a karo na 3.
Idan na zama shugaban kasa, Daga Kaduna zan rika gudanar da mulkina>>Inji Peter Obi

Idan na zama shugaban kasa, Daga Kaduna zan rika gudanar da mulkina>>Inji Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Peter Obi ya bayyana cewa, idan ya zama shugaban kasa, daga Kaduna zai rika gudanar da mulkinsa. Ya bayyana hakane a wajan wani taro a jihar Kaduna da ya halarta. Yace Kaduna ta yi kusa da Abuja sosai ta yanda idan ta kama shugaban kasa zai iya zuwa ya gudanar da taro a Kaduna har ya huta ya kuma koma Abuja. Yace idan ya zama shugaban kasa, zasu dawowa da Kaduna kwarjininta data rasa.
Kotu Ta daure Tsohon Akanta janar na Najeriya Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku tsawon shekaru 72 saboda satar Naira Miliyan N868.4

Kotu Ta daure Tsohon Akanta janar na Najeriya Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku tsawon shekaru 72 saboda satar Naira Miliyan N868.4

Duk Labarai
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta daure tsohon Akanta Janar na kasa, Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku bayan samunsa da laifin satar kudade da suka kai Naira Miliyan N868.4 Mai shari'a, Justice James Omotosho ne ya yanke masa hukuncin ranar Litinin bayan gamsuwa da hujjojin da aka gabatar masa kan zargin. An zargeshi da saka kudi a wasu asusun bankunan kamfanoni 4 wanda a baya ya karyata yace bai ma taba jin sunayen kamfanonin ba. Saidai daga baya ya amsa cewa lallai ya tura kudade zuwa asusun ajiyar kudi na wadannan kamfanonin. Kamfanonin sune kamar haka: Temeeo Synergy Concept Limited, Turge Global Investment Limited, Laptev Bridge, sai kuma Arafura Transnational Afro Limited. Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku a yanzu dai shekarunsa 64 a Duniya.
Da Duminsa: DSS sun sake kai samame gidan Tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami

Da Duminsa: DSS sun sake kai samame gidan Tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, DSS sun sake kai samame gidan tsohon Ministan shari'a Abubakar Malami a yau, Litinin. Samamen na DSS na zuwa jim kadan bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kaiwa Abubakar Malami ziyara gidan nasa. Rahotanni wanda Sahara Reporters ta ruwaito, tace DSS sun zagaye gidan na Malami yayin da Atiku ya kai masa ziyara, kuma bayan da Atikun ya tafi ne sai suka afka cikin gidan suka kori kowa daga ciki. Hakan na zuwane dai yayin da ake zargin gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da yunkurin murkushe 'yan Adawa kamin zaben shekarar 2027.
Da Duminsa: A karshe dai ICPC ta saka ranar da zata Gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai a gaban kotun Gwamnatin tarayya

Da Duminsa: A karshe dai ICPC ta saka ranar da zata Gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai a gaban kotun Gwamnatin tarayya

Duk Labarai
Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta bayyana cewa ta shirya tsaf dan gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a gaban babbar kotun tarayya dake Kaduna. Hukumar tace za'a gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne bisa zargin Almundahanar kudade, damfara da kuma amfani da ofishinsa ta hanyar da bata dace ba. Sanarwar tace za'a gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne tare da wani me suna  Joel Adoga ranar 24 ga watan Maris. Hakanan sanarwar tace akwai shari'a ta daban itama da za'a shigar da tsohon gwamnan Kadunan a babbar kotun jihar kaduna itama inda ake zarginsa da aikata ba daidai ba da ofishinsa da kuma karkatar da kudade.