Wednesday, September 16
Shadow
Ana zargin daya daga cikin yaran Farfesa Isa Ali Pantami da wallafa cewa idan me gidansu ya ci zabe zai hana Maulidi a jihar Gombe

Ana zargin daya daga cikin yaran Farfesa Isa Ali Pantami da wallafa cewa idan me gidansu ya ci zabe zai hana Maulidi a jihar Gombe

Duk Labarai
Ana zargin Daya daga cikin manyan yaran dan takarar Gwamnan jihar Gombe, Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami, watau Abba Pantami da yin wallafa a shafinsa na sada zumunta inda ya rubuta cewa, Idan Pantami ya ci zaben gwamnan jihar Gombe zai hana Maulidi. Screenshot na rubutun nasa yana ta yawo a kafafen sada zumunta inda ake ta sharhi akai. Inda a shafin Tauraron fina-finan Hausa Baba Sadiq aka fara ganin screenshot din wanda daga baya ya ci gaba da yaduwa. Zuwa yanzu dai Abba Pantami bai ce komai kan lamarin ba.
Gwamnatin jihar Benue ta kwace motoci 23 daga hannun Tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom

Gwamnatin jihar Benue ta kwace motoci 23 daga hannun Tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Benue ta kwace motoci 23 daga hannun Tsohon Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom bayan da ya kwashe su ya tafi dasu gidansa. An ga yanda aka yi Amfani da Janwai wajan dauke motocin daga gidan tsohon Gwamnan. Saidai Ortom yace wadannan motocin halas dinsa ne, Gwamnati ce ta mallaka masa https://twitter.com/Onsogbu/status/2098442953567940666
Bidiyon Abinda ya faru a masallacin Sheik Lukuwa

Bidiyon Abinda ya faru a masallacin Sheik Lukuwa

Duk Labarai
Matashi ya zo da sauri ya kama sahun gaba ta yadda ba zai yi nesa da liman ba sosai, bayan an idar da sallah sai Sheikh Lukuwa Sokoto ya juyo ya fuskanci mutanen cikin masallaci sai aka fara zuwa ana gaisawa da shi, caraf sai matashin nan ya je kusa da malam don su gaisa, nan ne ya samu damar yiwa malam abinda bai kamata ba InnaliLLAH wa'inna ilaihi rajiun! Cikin ikon Allah hanzarin da mutane suka yi wajan kaiwa malam dauki yasa matashin bai yi nasarar abinda yaje aikatawa ba, sai mutane suka kawo ɗauki aka kama shi kuma aka yi nasarar aika matashin lahira. Wannan shi ne abin da ya faru, muna fata wannan zai zama izina ga sauran malamai da limamai sannan ƴan agaji da masu tsaron malamai da limamai su ma su zama masu lura da irin wannan salo. Sannan rahoto ya zo cewa sauran masu i...
Wata Kirista ta yi kuskuren aika Naira Miliyan daya da dubu dari shidda Asusun ajiyar bankin Fastonta

Wata Kirista ta yi kuskuren aika Naira Miliyan daya da dubu dari shidda Asusun ajiyar bankin Fastonta

Duk Labarai
Wannan wata Kirista ce data yi kuskuren aikawa cocinta Naira Miliyan daya da dubu dari shidda da dubu arba'in da naira dari Biyu, 1,640,200. Ta fito kafafen sada zumunta tana ta kuka tana fadin cewa wallahi kudin bana sadaka bane, kudin aiki ne aka bata kuma mutane nata damunta. Tace idan akwai wanda yasan wanda ke kula da susun bankin cocin nata ya taimaka mata a musu magana su mayar mata da kudinta. https://twitter.com/dammiedammie35/status/2098555590125490381
Kalli Bidiyon: Yanda ta kaya bayan da wani matashi ya afkawa Sheikh Lukuwa

Kalli Bidiyon: Yanda ta kaya bayan da wani matashi ya afkawa Sheikh Lukuwa

Duk Labarai
Wani matashi da ya afkawa Sheikh Musa Lukuwa a masallacin juma'arsa ya gamu da ajalinsa a wajan mabiyan malamin. https://twitter.com/Bashar_G_Sokoto/status/2098453572606153138 Lamarin ya farune a masallacin malamin dake unguwar Mabera dake Jihar Sokoto bayan Sallar Juma'a. Rahotanni sun ce an sallami Malam daga asibitin da ak kaishi dan bashi kulawar gaggawa bayan faruwar lamarin.