An yiwa wayoyin Dangote da abokinsa Otedola kutse inda aka ce sai sun biya kudi za’a mayar musu
Rahotanni sun bayyana cewa, an yiwa wayoyin Attajiran Najeriya, Aliko Dangote dana Abokin Femi Otedola Kutse.
Masu kutsen kuma sun nemi sai an biya su makudan kudade kamin su mayarwa da attajiran iko da wayoyin nasu.
Rahoton wanda jaridar Thecable ta Ruwaito yace Sau daya aka yiwa Wayar Otedola kutse yayin da watar Dangote an masa kutse sau biyu.
Dangote da Otedola dai aminai ne wanda a wasu lokutan ma sukan kira kansu da 'yan uwa.








