DA ƊUMI-ƊUMI: An Yi Yunƙurin Hallãķa Laftanar Yerima Yau A Abuja
Wasu majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa wasu mutane da ba a san ko su waye ba, sanye da baƙaƙen kaya, cikin motocin Hilux da ba su da lamba sun bi sawun Yerima daga tashar mai ta NIPCO da ke kusa da Line Expressway zuwa Gado Nasco Way, a Abuja.
Sai dai, Yerima ya lura da yadda ake bin sa, sai ya yi dabara ya tsere wanda hakan ya ba shi damar gujewa waɗanda ake zargi da yunƙurin hallaka shin.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 6:30 na Yammacin yau, Lahadi, in ji majiyar, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
Laftanar A.M. Yerima dai Matashin jami’in Rundunar Sojan Ruwa ne ta Najeriya, wanda a kwanan nan ya yi taƙaddama da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike a kan wani fili da ake cece-kuce a unguwar Gaduwa, Abuja, lamarin da ya ɗauki hankulan ƴan Najeriya.








