Saturday, December 21
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Wutar Lantarkin Najeriya bata kara lalacewa ba a yau,Juma’a labarin karyane ake yadawa>>Inji Gwamnati

Wutar Lantarkin Najeriya bata kara lalacewa ba a yau,Juma’a labarin karyane ake yadawa>>Inji Gwamnati

Duk Labarai
Hukumar dake kulabda tsayuwar wutar Lantarki a Najeriya ta musanta cewa wutar lantarkin Najeriya ta sake lalacewa. A sanarwar data fitar ta kafar Twitter, tace a yi watsi da duk wani labari dake cewa wutar lantarkin Najeriya ta sake samun matsala. https://twitter.com/NationalGridNg/status/1854858514759405927?t=rMAr896DbG_IQl_kpeN_6g&s=19 A ranar Alhamis ne dai wutar lantarkin ta samu matsala a Najeriya wanda hakan ya jefa kasar cikin duhu.
Masu zanga-zanga sun je majalisar tarayya suna neman a kori shugaban NNPC Mele Kolo Kyari daga aiki

Masu zanga-zanga sun je majalisar tarayya suna neman a kori shugaban NNPC Mele Kolo Kyari daga aiki

Duk Labarai
Wasu kungiyoyin dake ikirarin fafutuka sun je majalisar tarayya suna neman a kori shugaban Kamfanin mai na kasa, NNPCL Mele Kolo Kyari daga aiki. Sun kuma nemi a yi bincike dan gano masu yiwa shirin gyaran matatun man fetur zagon kasa a Najeriya. Sun ce shugabancin Mele Kolo Kyari ya yiwa Matatun man fetur na Najeriya illa sosai. Shugaban kungiyar, Segun Adebayo, ya jawo hankalin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya jawa shugabancin kamfanin man fetur din na kasa, NNPCL kunne kan kasa su kara daukar wasu matakai da zasu kara jefa tattalin arzikin kasarnan cikin matsi. Kungiyar tace Najeriya zata iya tace man da za'a yi amfani dashi a cikin kasarnan amma saboda zagon kasa an hana hakan faruwa. Ta kara da cewa Misali ga Aliko Dangote ya bude matatar man fetur amma masu zago...
Kalli yanda wannan mutumin yawa kansa dan ya daina shan taba

Kalli yanda wannan mutumin yawa kansa dan ya daina shan taba

Duk Labarai
Wani mutum dan kasar Turkiyya da shan taba yawa katutu ya rasa yanda zai yi ya kulle kansa a cikin keji dan ya daina wannan dabi'a. Mutumin me suna Ibrahim Yucel, bayan ya kulle kansa ya baiwa matarsa makullin inda take budeshi kawai idan zai ci abinci. Saidai zuwa yanzu ba'a san ko hakan ya taimaka masa wajan cimma burinsa ba. Rahotanni sun bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan da cutar dajin huhu ta kashe mahaifinsa.
Shugaban ‘Yansandan Najeriya ya bayar da umarni ga ‘yansanda su daura bakin kyalle dan nuna Alhinin rayuwar shugaban sojoji

Shugaban ‘Yansandan Najeriya ya bayar da umarni ga ‘yansanda su daura bakin kyalle dan nuna Alhinin rayuwar shugaban sojoji

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, IGP Kayode ya bayar da umarni ga 'yansandan kasarnan da su daura bakin kyalle na tsawon kwanaki 7 dan nuna alhinin rasuwar shugaban sojoji Lt. Gen. Taoreed Lagbaja. Kakakin 'yansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai. Yace wannan matakine da aka dauka dan girmama tsohon shugaban sojojin da kokarin da ya nuna wajan yaki da matsalar tsaro.
Muna matukar godiya da hakuri da kuke yi da wahalar da tsare-tsaren gwamnatin mu suka jefa ku ciki amma yanzu lamura sun fara Gyaruwa>>Gwamnatin Tarayya ga ‘yan Najeriya

Muna matukar godiya da hakuri da kuke yi da wahalar da tsare-tsaren gwamnatin mu suka jefa ku ciki amma yanzu lamura sun fara Gyaruwa>>Gwamnatin Tarayya ga ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin Tarayya ta yiwa 'yan Najeriya godiya bisa hakurin da suke yi da matsin rayuwa da suka shiga saboda tsare-tsaren gwamnatin. Hakan ya fito ne daga bakin ministan kudi, Wale Edun inda yake ganawa da 'yan majalisar tarayya. Yace 'yan Najeriya sun cancanci yabo bisa hakuri da juriya da suka nuna inda gashi yanzu har an kawo matakin moriyar wadannan gyare-gyaren. Ministan yace manya-manyan gyare-gyaren da suka yi sune cire tallafin man fetur da cire tallafin dala wanda kuma yanzu an fara ganin nasarar wannan mataki nasu.
Za mu kawo ƙarshen Lakurawa cikin ƙanƙanin lokaci- Hedkwatar tsaro

Za mu kawo ƙarshen Lakurawa cikin ƙanƙanin lokaci- Hedkwatar tsaro

Duk Labarai
Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da ɓullar ƙungiyar lakurawa waɗanda suke tayar da zaune tsaye a tsakanin jihohin Sokoto da Kebbi. Daraktan watsa labarai na hedkwatar ne ya tabbatar da hakan a Abuja, kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito, inda ya ƙara da cewa suna da tabbacin ɓullar ƙungiyar a Sokoto da Kebbi. Sai dai ya ƙara cewa ƙungiyar ba za ta yi wani tasiri ba, domin a cewarsa sojojin Najeriya a shirye suke, kuma za su ga bayansu cikin ƙanƙanin lokaci. Lakurawa wata ƙungiya ce ta ƴanbindiga da suka fara addabar mutanen Sokoto da Kebbi, kuma sun fito ne daga ɓangaren yankin Sahel da ya ƙunshi ƙasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban na Sahel.
Likitocin Kano sun dakatar da shiga yajin aiki

Likitocin Kano sun dakatar da shiga yajin aiki

Duk Labarai
A jihar Kano, ƙungiyar likitoci ta umarci likitocin jihar su koma bakin aiki bayan janye yajin aikin da aka wayi gari da shi a asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad a ranar Alhamis. Likitocin dai sun shiga yajin aikin ne bayan cikar wa’adin sa’o’i 48 da ƙungiyar ta baiwa gwamnan jihar, na ya kori kwamishiniyar jin ƙai ta jihar, Amina Abdullahi HOD, bisa zargin cin zarafin wata likita a asibitin, zargin da ta ce musanta. Duk da cewa likitocin sun janye yajin aikin amma ƴan sa’o’in da aka shafe babu likitoci a asibitin na Murtala Muhammad har an ga tasirinsa, inda ya shafa majinyata.
An yi hasashen ƴan Najeriya miliyan 33 za su yi fama da yunwa a 2025

An yi hasashen ƴan Najeriya miliyan 33 za su yi fama da yunwa a 2025

Duk Labarai
Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa yunwar da ake fama da ita a Najeriya zai iya tsananta a shekarar 2025, inda aka yi hasashen cewa aƙalla mutum miliyan 33 ne za su iya shiga yunwa a shekarar ta baɗi. Ƴan Najeriya a yanzu sun kai kusan miliyan 223.8. A rahoton, wanda Cadre Harmonisé ta yi a ƙarƙashin kulawar gwamnatin tarayya, da haɗin gwiwar shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ne ya bayyana hakan, inda rahoton ya yi hasashen cewa ƴan ƙasar aƙalla miliyan 33.1 ne za su fuskanci yunwa. Rahoton ya ta'allaƙa hasashen ne kan yanayin taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar da hauhawar farashin kayayyaki da sauyin yanayi da rikce-rikice a wasu yankuna na arewacin ƙasar. Rahoton ya ƙara da cewa tsakanin Oktoba zuwa Disamban 2024, kimamin mutum miliyan 25.1 ake hasashen za...