Hukumar jirgin kasa ta Najeriya ta sanar da rage kudin tikitin jirgin da kaso 50 saboda bukukuwan karshen shekara
Hukumar jirgin kasa ta Najeriya, The Nigerian Railway Corporation ta sanar da rage farashin Tikitin jirgin da kaso 50 saboda bukukuwan karshen shekara.
Hukumar tace ragin zai fara aiki ne a yau, Talata.
A ranar 25 ga watan Disamba ne za'a yi bikin Kirsimeti sannan akwai bikin karshen shekara na 1 ga watan Janairu wanda duka Gwamnati ta bayar da hutu.








