Wednesday, January 14
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Da Duminsa: FIFA tace ta karbi Korafin Najeriya akan Dr. Congo kuma tana bincike akai

Da Duminsa: FIFA tace ta karbi Korafin Najeriya akan Dr. Congo kuma tana bincike akai

Duk Labarai
Rahotanni da muke samu a yanzu haka na cewa, Hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA ta karbi korafin Najeriya akan Dr. Congo kuma tace tana bincike akan lamarin. Najeriya ta shigar da korafin cewa, kasar Dr. Congo ta yi amfani da 'yan wasa masu kasashe biyu a wasan da suka buga da Najeriya wanda hakan ya sabawa dokar kasar. Idan Najeriya ta yi nasara a wannan Shari'ar, akwai yiyuwar zata buga gasar cin kofin Duniya na shekarar 2026.
Da Duminsa:’Yansanda sun mamaye Otal din Azir da Azir Arena mallakin Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami dake tsare a hannun EFCC

Da Duminsa:’Yansanda sun mamaye Otal din Azir da Azir Arena mallakin Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami dake tsare a hannun EFCC

Duk Labarai
Rahotanni sun ce an ga 'yansanda sun mamaye Otal din Azir da Azir Arena dake jihar Sakkwato wanda mallakin tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami ne. Malami dai yana hannun hukumar EFCC tana bincikensa. Ana zarginsa da Almundahanar kudade masu yawa. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/2002726485363470604?t=8ZQ3Nvma9rAUyTnPU9_1YA&s=19
Kalli Bidiyon: Na je wata makarantar Allo, nawa Malaminsu Albashin Naira dubu 50 duk wata>>Inji Peter Obi

Kalli Bidiyon: Na je wata makarantar Allo, nawa Malaminsu Albashin Naira dubu 50 duk wata>>Inji Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa, na jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, ya je wasu makarantun Allo inda ya tambayi nawa ake biyan malaman? Yace Ya yiwa malaman Albashin Naira 50,000. Sannan kuma ya dauki malaman koyar da Turanci da Lissafi da kimiyya da fasaha suma ya musu Albashin Naira dubu 50,000. Ya bayyana cewa, yana da yakinin yaran zasu sama masu amfani anan gaba. https://twitter.com/dammiedammie35/status/2002659483143831905?t=jl551SBr27lgrN2dqstf6w&s=19
A’isha Buhari ta sake bayyana wani abin mamaki game da rayuwar Buhari da ya sa mutane rike baki

A’isha Buhari ta sake bayyana wani abin mamaki game da rayuwar Buhari da ya sa mutane rike baki

Duk Labarai
Matar tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Hajiya A'Isha Buhari ta bayyana cutar da tawa tsohon shugaban Katutu har ya rasu. Ta bayyana cewa, Shugaba Buhari yana fama da matsalar ciwon Sanyi. Tace kuma ciwon ya samo asali ne daga aikinsa na soja lokacin yana matashi, suna shiga daji, kaya na bushewa a jikinsa bayan sun jike. Sannan da sanyin AC, watau na'urar sanyaya daki ga kuma tsufa duk sun tarar masa a jiki. Hakanan ta kawo cewa, Tsohon shugaban ya sha taba lokacin yana matashi wanda hakan ma ya taimaka wajan rashin lafiyar tasa. Hajiya A'isha Buhari dai ta yi maganganu da yawa akan Marigayi Shugaba Buhari da suka baiwa mutane mamaki, wasu na ganin cewa bai kamata ta yi su ba.