Tuesday, March 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Barawo Ya Sace Wayar Wannan Malamain, Bayan Kwana Biyu Kuma Barawon Ya Mutu, Shine Ake Zargin Malamain Da Hannu A Mutuwar Barawon

Barawo Ya Sace Wayar Wannan Malamain, Bayan Kwana Biyu Kuma Barawon Ya Mutu, Shine Ake Zargin Malamain Da Hannu A Mutuwar Barawon

Duk Labarai
BA FADA DA MALAM BA… Barawo Ya Sace Wayar Wannan Malamain, Bayan Kwana Biyu Kuma Barawon Ya Mutu, Shine Ake Zargin Malamain Da Hannu A Mutuwar Barawon Saidai a hirar da aka yi da Malamin ya ce shi ba shida hannu a mutuwar domin hasalima ya yafewa barawon wayarsa da ya sace masa. Malamin ya kuma kara da cewa duk wanda ya ce shine ya kashe barawon wayan nasa, to shima ya jira nasa. Me za ku ce?
Taufa Kalli Yanda wani dan Kripto ya lalata kwamfutarsa da sauran kayan amfaninsa saboda haushin Kasuwa ta lalace, yace ya sayar da komai

Taufa Kalli Yanda wani dan Kripto ya lalata kwamfutarsa da sauran kayan amfaninsa saboda haushin Kasuwa ta lalace, yace ya sayar da komai

Duk Labarai
Wani Dan Kripto ya bayyana rashin jin dadinsa da yanda kasuwar ta lalace a yanzu inda ya bayyana cewa ya sayar da duk wani abu na Cryptocurrency daya mallaka. Ba wannan kadai ba kuma ya sanar da lalata Kwamfutatsa da sauran kayan da yake amfani dasu. Wasu sun bashi baki inda akai masa jaje yayin da wasu suka ce basu ma yadda dashi ba.
Wata mata me suna Salamatu ta kkàshe Mijinta a jihar Bauchi ta hanyar daba masa wuka

Wata mata me suna Salamatu ta kkàshe Mijinta a jihar Bauchi ta hanyar daba masa wuka

Duk Labarai
Wata mata a jihar Bauchi me suna Salamatu Danjuma me kimanin shekaru 25 ta kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka. Lamarin ya farune a garin Nadago dake karamar hukumar Tafawa Balewa. Kakakin 'yansandan jihar, Ahmed Wakil ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin inda yace rikici kan rikon diyarsu ne ya jawo fadan da ya kai ga matar ta dabawa mijinta wuka. An kai mijin Asibiti inda likitoci suka tabbatar da ya mutu. Kwamishinan 'yansandan jihar,Auwal Mohammed ya bayar da umarnin yin bincike sosai akan lamarin.
Dalibin jami’a ya nutse ya mutu a ruwa bayan da aka saka masa Naira 300 idan ya tsallake ruwan da iyo

Dalibin jami’a ya nutse ya mutu a ruwa bayan da aka saka masa Naira 300 idan ya tsallake ruwan da iyo

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, dalibin jami'ar Federal University, Otuoke jihar Bayelsa ya nutse a ruwa bayan da suka yi caca shi da abokansa. Dalibin sun yi gaddama da abokansa kan cewa, ba zai iya tsallake wani ruwa bane da iyo inda shi kuma yace zai iya. Anan ne sai suka saka Naira Dari uku kowannensu shi da abokansa. Ya shiga ya fara iyo a cikin ruwan sai suka ga ya nutse, har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba'a gano gawarsa ba. Rahoton jaridar Punchng ya bayyana cewa an yi kokarin tuntubar hukumar makarantar dan jin ta bakin kakakin makarantar Ms Mercy Ekott, saidai an ta kiran wayarta amma taki dagawa. An kuma tuntubu kakakin 'yansandan jihar, Mr Musa Mohammed inda yace bai san da maganar ba.
An kama matashi da ya kkàshè Budurwarsa

An kama matashi da ya kkàshè Budurwarsa

Duk Labarai
Mahukunta a jihar Legas sun kama wani mutum me suna Gbolahan Adebayo bida zargin kashe budurwarsa. Adebayo dan shekaru 23 ya daki budurwarsa me shekaru 25 har ta mutu. Lamarin ya farune a ranar 21 February 2025 kamar yanda Daily Post ta ruwaito. Kakakin 'yansandan jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace abin ya farune a Ijedodo, Isheri-Osun dake jihar. Wani makwabci daya shaida lamarin yace ya ji Adebayo na dukan budurwar tasa kuma da aka leka aka tarar bata motsi, saidai zuwa yanzu ba'a san dalilin da yasa ya kashe budurwar tasa ba. Tuni dai aka kai ta Asibiti inda likitoci suka tabbatar da ta mutu.
Haduwar Mawakiyar Najeriya, Ayra Starr da shahararriyar me yin fina-finan bàtsà Mìa Khàlìfà ya jawo cece-kuce

Haduwar Mawakiyar Najeriya, Ayra Starr da shahararriyar me yin fina-finan bàtsà Mìa Khàlìfà ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Tauraruwar Mawakiyar Najeriya, Ayra Starr ta hadu da shahararriyar me fina-finan batsa, watau Mia Khalifa. Bidiyon haduwarsu suna hira ya karade kafafen sada zumunta inda wasu ke tambayar me ya hadasu? Mia Khalifa dai wadda asalinta 'yar kasar Lebanon ce ta bayyana daina yin fina-finan batsa, inda ta koma shafin Onlyfan wanda saidai idan mutum nason ta mai bidiyon ta tsirara ya biya kudi ta masa.
Bidiyo:Na Tuba na daina Yada Badala>>Inji ‘Yar Tiktok, Shalele

Bidiyo:Na Tuba na daina Yada Badala>>Inji ‘Yar Tiktok, Shalele

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok da ta shahara sosai wajen yada badala da maganganun batsa Shalele ta bayyana cewa ta tuba. Shalele wadda har bidiyoyinta tsirara sun yadu sosai tace daga yau ta daina duk wani na ba daidai ba da ya sabawa Addini da Al'ada. https://www.tiktok.com/@drshalele2/video/7473392723249106231?_t=ZM-8uCdD1ruVtv&_r=1 Da yawa sun jinjina mata kan wannan mataki data daukarwa rayuwarda.
Dan Allah ku gayawa El-Rufai ya shafa min Lafiya, Ni Aiki nane a gabana ba cece-kuce a gidajen watsa labarai ba>>Nuhu Ribadu

Dan Allah ku gayawa El-Rufai ya shafa min Lafiya, Ni Aiki nane a gabana ba cece-kuce a gidajen watsa labarai ba>>Nuhu Ribadu

Duk Labarai
Ba Zan Yi Musayar Yawu Da Nasir El-Rufai Ba, Cewar Nuhu Ribadu "An ja hankalina zuwa ga hirar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi da kafar yada labarai da yammacin ranar Litinin. Da ba don gudun kada na yi shiru a gaskata maganganunsa ba, da na yi watsi da shi. Saboda na fi shagaltuwa da tarin aiyukan da ke gabana,fiye da tanka ire-iren su Nasir El-Rufai a kafafen yada labarai. Duk da cin zarafi da aibata ni da Nasiru yake yi, hakan bai sa na taba fadin wani mummunan abu akansa ba a ko’ina. Ba don komai na ki aibata shi ba sai don mutunta zumuncin da ke tsakaninmu da kuma abotar mu ta baya, don haka abinda ban yi tun a baya ba, ba zan fara yanzu ba. Sai dai ina kira ga jama'a da su yi watsi da ikirarin El-rufai akaina Bari na kankare muku shakku in fadi...
Nuhu Ribadu na son zama shugaban kasa a 2031 bayan Tinubu ya gama shiyasa yake son bata min suna>>El-Rufai

Nuhu Ribadu na son zama shugaban kasa a 2031 bayan Tinubu ya gama shiyasa yake son bata min suna>>El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, Nuhu Ribadu na son zama shugaban kasa a shekarar 2031 bayan Tinubu ya gama Mulki. Yace shiyasa ma Nuhu Ribadun ya hada kai da gwamnan Kaduna na yanzu, Malam Uba Sani dan bata masa suna. El-Rufai ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Inda ya kara da cewa amma kokarin na bata masa suna yana basu wahala.
Da Tinubu ya zarce a 2027 gara ma koda daga kudu ne a sake samun wani ya zama shugaban kasa>>El-Rufai

Da Tinubu ya zarce a 2027 gara ma koda daga kudu ne a sake samun wani ya zama shugaban kasa>>El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa gara wani daga kudu ya sake zama shugaban kasa da Tinubu ya sake zama shugaban kasa a shekarar 2027. El-Rufai ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Yace bai da tabbacin nan da lokacin zaben 2027 ko zai ci gaba da dama a Jam'iyyar APC. El-Rufai ya zargi Tinubu da nada yaransa mafi yawanci yarbawa a mukaman siyasa.