Wannan wata ce data maqale a cikin kujerar daukar hoto a yayin da suka je shagon me daukar hoton.
Lamarin ya dauki hankula a kafafen sada zumunta.
https://twitter.com/i/status/2058771523100459454
Wani Bidiyo ya watsu a kafafen sada zumunta inda aka ga anawa wani Attajiri sihirin Mallaka.
Wani Bokane ke yin Sihirin inda aka ji yana kiran sunan Mutumin yana cewa sai ya baiwa wata mata kudaden da ya mata alkawari kamin ya samu kwanciyar Hankali.
https://twitter.com/i/status/2058992593690628213
A jiyane, Dan tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai ya bayyana cewa, Gwamna Uba Sani ya rika bin matan mahaifinsa yana rokonsu gwiwoyi kasa kan su roki mahaifinsa ya tsayar dashi takarar Gwamna.
Ya kara da cewa Gwamnan ya kuma rika bin na kusa da Mahaifinsa yana basu kudi dan suwa mahaifinsa magana ya tsayar dashi takarar.
Yace hakanan har yayan mahaifinsa ma saida Uba sani ya rika bi yana roko dan a tsayar dashi takarar Gwamna.
https://twitter.com/i/status/2058771249858310214
Saidai mahaifiyar Bashir, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai, ta karyatashi inda tace ba'a yi haka da ita ba.
https://twitter.com/i/status/2058841164384444747
Bayan fitar Bidiyon Update na Tauraruwar Tiktok, Babiana wanda ya karade shafukan zumunta a kwanannan.
Bidiyon guda Biyu ne, daya Mintuna 6, dayan kuma sakan 30.
Saidai Sadiya Haruna tace Bidiyon na da yawa, sun fi 30 amma ta bayar da hakuri tace a daina sakinsu haka.
Wasu dai na zargin Sadiya Haruna ce ta saki Bidiyon saboda rashin jituwar dake tsakaninta da Babiana.
https://www.tiktok.com/@sayyada_sadiya_haruna/video/7642368014502858001?_r=1&_t=ZS-96fnjjQaSrg
Wannan wani matashi ne da rahotanni suka bayyana cewa, ya sha na jaki bayan da ya shiga cikin kasuwa a Kano yana tallata Shugaba Tinubu.
An ga yanda matasa suka masa rubdugu inda daga karshe dai tserewa yayi.
Da yawa dai sun rika masa Allah kara
https://twitter.com/i/status/2058639028107329546
Sabon Fim din Turanci na Tauraruwar fina-finan Hausa, Fatima Hussain, wadda aka fi sani da Maryam Labarina ta shirya me suna Ammy and Dammy ya jawo cece-kuce sosai.
Tuni wasu suka fara sukar fi din da bayyana cewa, wai ana tabe-tabe tsakanin maza da mata wanda hakan bai dace ba.
Bayan kallon Tallar fim din, Wakilin Hutudole ya lura cewa, tabbas an dan yi tabe-tabe a fim din wanda a al'ada da addinin Arewacin Najeriya hakan bai dace ba.
https://www.tiktok.com/@refiningreflections/video/7643491997919038738?_r=1&_t=ZS-96ebIspdDhy
https://www.tiktok.com/@manyan_mata_series/video/7643192948447874324?_r=1&_t=ZS-96ebmZn8hQV
Wata mawakiya Bahaushiya Ta bayyana inda ta dakko salon waka irin na turawa.
An ganta tana waka a bandaki yayin da take wanka babu kaya a jikinta.
Lamarin ya dauki hankula sosai.
Da yawa dai sun ce hakan bai dace ba.
https://www.tiktok.com/@batulayaramanacemana/video/7641094105384226069?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7641094105384226069&source=h5_m×tamp=1779229726&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7625183675001341712&share_link_id=db037f47-b1a0-4ee9-98c8-83bf8...
Hukumar HISBAH ta jihar Kebbi ta sanar da kama wani Kwarto a cikin dakin matar aure a boye a cikin jakar Ghana Must Go.
Lamarin ya farune ranar Litinin, 18 ga watan Mayu a unguwar Badariyya dake Birnin Kebbi.
Jama'ar Unguwane suka lura da mutumin ya shiga gidan matar auren inda suka gaggauta sanar da hukuma.
Daraktan HISBAH na jihar, Sirajo Kamba ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yanda daily Trust ta ruwaito.
Yace da jami'an sa suka je gidan suka nemi izinin shiga, matar taki amincewa amma da aka dade ana turjiya sai ta amince.
Aikuwa da bincike yayi tsanani sai ga Kwarto a cikin jakar Ghana Must Go.
An kamasu duka aka tafi aka fara bincike inda duka suka amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa na soyayya.
Kamba yace za'a gurfanar dasu gaban kotu domin yanke musu...
Wasu 'yan mata da aka rika bayyana cewa daga Arewa suka fito sun dauki hankula bayan wata rawa da suka yi data jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Da yawa dai sun ce rawar da suka yi bata kamata ba musamman ganin cewa sun saka kayan dake nuna kamala.
https://twitter.com/i/status/2056010567135981797
Wasu kuma sun rika bayyana cewa, Shiga me kamala ba ita ke nuna mutum na da tarbiyya ba.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa idan babba bai kama girmansa ba, Karami ba zai ji kunyar shi ba.
Gwamnan ya bayyana hakane akan takaddamar dake tsakaninsa da Tsohon Maigidansa, Kwankwaso wanda tun bayan da ya bar Jam'iyyar NNPP zuwa APC dangantaka ta yi tsami tsakaninsu.
Abba ya bayyana mamakin yanda Kwankwaso dake da shekaru 69 yake ce masa yaro saboda yana da shekaru 63.
https://twitter.com/i/status/2056469075836989481