Saturday, January 11
Shadow

Duk Labarai

An min Wahayi cewa, za’a yi yunkurin kkashe shugaban kasa ta hanyar bashi guba amma zai tsallake, sannan wani gwamna zai muttu a 2025>>Inji Fasto Ayodele

An min Wahayi cewa, za’a yi yunkurin kkashe shugaban kasa ta hanyar bashi guba amma zai tsallake, sannan wani gwamna zai muttu a 2025>>Inji Fasto Ayodele

Duk Labarai
Babban fasto, Primate Ayodele ya bayyana abubuwan da zasu faru a shekarar 2025 kamar yanda ya saba yi duk shekara inda yake ikirarin an masa wahayi. Faston yace wasu daga cikin abubuwan da aka masa wahayi shine cewa za'a saki shugaban kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra watau, Nnamdi Kanu, sannan matsin rayuwa zai karu a shekarar ta 2025. Yace ya kuma gano cewa wani gwamna zai mutu, sannan za'a yi yunkurin kashe wani shugaban kasa ta hanyar zuba masa guba amma zai tsallake, saidai be bayyana kowane shugaban kasa bane. Ya kuma za'a samu matsalar kisan jami'an tsaro na FBI da CIA na kasar Amurka.
A Yanzu Haka Za A Iya Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Sadaki, Inji Limamin Masallacin Albabello Dake Zaria

A Yanzu Haka Za A Iya Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Sadaki, Inji Limamin Masallacin Albabello Dake Zaria

Duk Labarai
A Yanzu Haka Za A Iya Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Sadaki, Inji Limamin Masallacin Albabello Dake Zaria Malamin ya ce "kamar yadda ya tabbata a mazhabar Imam Malik za a iya biyan rub'u dinar ko darhami uku, inda dubu talatin ce kiyasin darhami uku", Inji- Imam Dr. Hamza Assudaniy Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Albabello Zaria.
Shugaban Najeriya, Tinubu ya shiga jerin shuwagabannin kasashen Duniya mafiya rashawa da cin hanci inda ya zo a matsayi na 3

Shugaban Najeriya, Tinubu ya shiga jerin shuwagabannin kasashen Duniya mafiya rashawa da cin hanci inda ya zo a matsayi na 3

Duk Labarai
Wani rahoto da ya bayyana, ya nuna shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaba Mafi rashawa da cin hanci inda ya zo a matsayi na 3 a Duniya. Wata kungiya me suna, (OCCRP) ce ta bayyana hakan. Ta kuma samu wanna sakamako ne bayan da ta nemi a yi zabe dan fitar da mutane mafiya rashawa a Duniya. Kungiyar ta hada da manyan 'yan Jarida ne da 'yan fafutuka dan kare hakkin al'umma. Shugban kasar Kenya, William Ruto ne ya zo na daya sai kuma shugaban kasar Indonesia, Joko Widodo ya zo na uku. Hambararren Shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad ne ya zamo gwarzon shekara.
Ban yi wata murna sosai da zama shugaban kasa ba, saboda irin barnar da na iske n yiwa Najeriya>>Tinubu

Ban yi wata murna sosai da zama shugaban kasa ba, saboda irin barnar da na iske n yiwa Najeriya>>Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, bai yi wata murna da zama shugaban kasa ba bayan da ya iske irin barnar da aka yiwa Najeriya. A bayyana hakane ga kakakin majalisar dattijai, Godwill Akpabio. Akpabio ne ya bayyana hakan a wajan rabon kayan da yayi ga mutanen mazabarsa wanda suka hada da kayan abinci da ababen hawa da sauransu a jiharsa ta Akwa-Ibom. Yace wata rana ya taba tabayar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan shin ko yayi murnar zama shugaban kasa kuwa lura da irin barnar da ya iske tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele yawa kasar? Sai shugaba Tinubu yace masa murna kadan yayi. Bai san barnar da akawa Najeriya ta kai haka ba. Akpabio ya kara da cewa, ya gayawa shugaban kasar cewa, yayi imanin kamar yanda ya gyara Legas, Itama Na...
Matasa dake tsakanin shekaru 21 zuwa 30 ne suka fi sayen maganin karfin maza>>Ji Illar da yake a jikin mutum

Matasa dake tsakanin shekaru 21 zuwa 30 ne suka fi sayen maganin karfin maza>>Ji Illar da yake a jikin mutum

Duk Labarai
Bincike ya nuna cewa, matasa dake tsakanin shekaru 21 zuwa 30 ne a Najeriya suka fi amfani da maganin karfin maza . Yawanci ana sayen magungunan kara karfin maza ne dan samun kuzari da jin dadin jima'i. Saidai da yawa daga cikin magungunan da ake sayarwa din basu da rijista hukukomin lafiya na kasa basu tantance su ba, hakanan kuma mafi yawan masu sayar da magungunan ma basu da ilimi akan harkar maganin. Hakan yasa ake samun matsalar magungunan su rika bayar da illa ga lafiyar dan adam inda akan samu matsalar mazaje na mutuwa yayin jima'i.
Kada ku yadda da sabuwar dokar haraji>>Sanata Ndume ya gayawa sarakuna

Kada ku yadda da sabuwar dokar haraji>>Sanata Ndume ya gayawa sarakuna

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno yayi kira ga sarakunan dake karkashin mazabarsa da kada su yadda da sabuwar dokar haraji ta shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ya bayyana hakane a yayin da ya kai ziyara Masarautar Askira, inda yace dalilinsa na kin amincewa da dokar harajin shine wahalar da mutane ke ciki, dan hakane yake kira da sarakunan da suma kada su amince da ita. Yayi kira ga matasa da su tashi su rungumi harkar noma inda yace a daina dogaro da gwamnati da Albashi dan kuwa albashin Naira dubu 70 ba zai sayi buhun shinkafa ba dake Naira dubu 100 ko buhun wake dake Neman kaiwa Naira dubu dari 200. Ya jinjinawa mutanen garin Gwoza saboda jajircewar da suka nuna duk da matsalar tsaron da suke fama da ita inda yace babu yanda za'a yi a rika kawo musu hare-hare ba tare da masu b...
‘Yan Najeriya na cikin wahala a matsin rayuwa, Rabon kayan abinci ba shine magani ba>>Inji Tsohon Kakakin Majalisar Dattijai, Ahmad Lawal

‘Yan Najeriya na cikin wahala a matsin rayuwa, Rabon kayan abinci ba shine magani ba>>Inji Tsohon Kakakin Majalisar Dattijai, Ahmad Lawal

Duk Labarai
Tsohon kakakin majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya bayyana cewa, mutane na cikin matsin rayuwa kuma rabon kayan abinci ba shi bane mafita. Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta bakin kakakinsa, Ezrel Tabiowo bayan da ya je mazabarsa dake jihar Yobe ya raba kayan tallafi. Yace kamata yayi a samarwa mutane hanya da zasu dogara da kansu amma rabon abinci zai kawo sauki ne kawai na dan lokaci wanda kuma wahalar zata ci gaba. Saidai yace kamin su kai ga wancan matsayi, su dake da halin bayarwa zasu ci gaba da bada tallafin dan saukakawa mutane rayuwa. Yayi kira ga masu rike da madafan iko dasu dauki matakan da zasu kawowa Al'umma saukin rayuwa.