Saturday, February 28
Shadow

Duk Labarai

Kalli Yanda matan da ake zargin an baiwa kudi dan su fito tarbar shugaba Tinubu a Kaduna ke kulle fuskokinsu basu son kyamara ta daukesu hoto

Kalli Yanda matan da ake zargin an baiwa kudi dan su fito tarbar shugaba Tinubu a Kaduna ke kulle fuskokinsu basu son kyamara ta daukesu hoto

Duk Labarai
Wadannan wasu matane da ake zargin an baiwa kudi dan su fito su tarbi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a Kaduna. Saidai sun ki yadda kyamara ta dauki fuskokinsu inda suke kulle fuskokin. Tsohuwar hadimar Shagaban kasa, Lauretta Onochie ce ta wallafa hoton inda tace an tursasa matan ne su yi tallar Tinubu. https://twitter.com/Laurestar/status/1969359202163261601?t=8t3C8PF-UvpUXRXcCRglAw&s=19
Kalli Bidiyo: Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Gayu ta zama ta farko a masana’antar data mallaki wayar iPhone 17 Pro ta sama da Naira Miliyan 2

Kalli Bidiyo: Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Gayu ta zama ta farko a masana’antar data mallaki wayar iPhone 17 Pro ta sama da Naira Miliyan 2

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Gayu ta kasance jaruma ta farko a masana'antar da ta fara bayyana sayen sabuwar wayar iPhone 17 pro. Wayar dai wadda kamfanin Apple ya sanar da fitowarta a makon da ya gabata itace ake ta magana a gari musamman tsakanin masoya wayoyi. Farashin wayar ya haura Naira Miliyan 2 inda a wani gurin ma ana samunta akan Naira 2,990,000. An ga Jaruma Ummi Gayu a wani Bidiyo da ya watsu sosai tana nuna wayar a hannunta. https://www.tiktok.com/@yar.fulani.yola/video/7551857713538403605?_t=ZS-8zsbi5ZEU7t&_r=1
Mutanen Kaduna sun ki fitowa su tarbi Tinubu shine suka samo yara ‘yan makaranta suka zuba akan Titi>>Inji Tsohuwar Hadimar Shagaban kasa, Lauretta Onochie

Mutanen Kaduna sun ki fitowa su tarbi Tinubu shine suka samo yara ‘yan makaranta suka zuba akan Titi>>Inji Tsohuwar Hadimar Shagaban kasa, Lauretta Onochie

Duk Labarai
Tsohuwar hadimar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta bayyana cewa, ziyarar da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai jihar Kaduna bata yi Armashi ba. Ta godewa mutanen Kaduna saboda kin fitowa su tarbi shugaban kasar inda tace sai yara aka samo aka zuba akan titi. Ta bayyana hakane a shafinta na X. Ta kara da cewa, wannan sakamakon mulki da rashin bin doka kenan. https://twitter.com/Laurestar/status/1969161660553187344?t=S78sFGCVGhA-gpmwqQO5iA&s=19
Ka wallafa Sunayen mutanen da Gwamnatinka tace ta baiwa Tallafin Naira dubu ashirin da biyar duk wata>>Kungiyar Yarbawa ga Shugaba Tinubu

Ka wallafa Sunayen mutanen da Gwamnatinka tace ta baiwa Tallafin Naira dubu ashirin da biyar duk wata>>Kungiyar Yarbawa ga Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Wata Kungiyar Yarbawa me suna Ìgbìnmó Májékóbájé Ilé-Yorùbá ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya wallafa sunayen mutanen da gwamnatinsa tace ta rika baiwa tallafin Naira dubu 25 duk wata. Kungiyar ta bakin shugabanta, Olusola Badero tace wannan maganar duk farfaganda ce. Tace ko da da gaske an bayar da wannan tallafin, idan aka duba, za'a ga cewa yawanci 'yab jam'iyyar APC ne. Tace dan haka a wallafa sunayen mutanen da aka baiwa tallafin da jihohin da suka fito. Kungiyar tace ko da ma an bayar da tallafin da gaske, Naira 25,000 a wata ba zata iya ciyar da iyali ba, saboda buhun shinkafa ya haura Naira 70,000. Kumgiyar tace tun da shugaba Tinubu ya hau mulki mutane a shiyyar Yarbawa suka fada yunwa da talauci inda da yawa sun koma roko kamin su samu abinci....
Kalli Bidiyon dandazon jama’ar da suka Tarbi Shugaba Tinubu a Kaduna, wasu sun ce ko Buhari sai haka

Kalli Bidiyon dandazon jama’ar da suka Tarbi Shugaba Tinubu a Kaduna, wasu sun ce ko Buhari sai haka

Duk Labarai
Mutane da yawa ne suka fito suka tarbi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a ziyarar da ya kai Jihar Kaduna. Shugaba Tinubu ya je jihar Kadunane halartar daurin auren dan sanata Abdulaziz Yari, sannan ya kaiwa matar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari watau Hajiya A'isha Ziyara. https://twitter.com/HBMayana_/status/1969121724374409254?t=f8p24RUXvNk9tsGG1mvYjQ&s=19