Koda mun gyara wutar Najeriya kara lalacewa zata yi saboda injinan wutar sun tsufa>>TCN
A yayin da matsalar wutar lantarki ta zama ruwan dare a Najeriya, Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin yin gyaran gaba dayan matsalar wutar.
Gyaran dai zai dauki nan da zuwa watanni 6 har shekara 1.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan inda yace a canja injinan wutar lantarkin da magance matsalar wutar gaba daya.
Kakakin Ministan, Bolaji Tunji ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Dama a baya an kafa wani Kwamiti da ya gano matsalolin wutar wanda suka hada da tsaffin injina da rashin kula da injinan yanda ya kamata da kuma karancin Injinan da zasu samarwa Najeriya ingantacciyar wutar lantarkin.
Kwamitin dai ne ya bayar da shawarar yanda za'a kawo karshen matsalar wutar wanda ministan yace a gaggaura yin amfani da shawarar kwamitin.