Friday, January 17
Shadow

Duk Labarai

Shugaban ‘yansandan Najeriya ya bayar da umarnin yin bincike kan yanda aka tsare kananan yara masu zàngà-zàngà

Shugaban ‘yansandan Najeriya ya bayar da umarnin yin bincike kan yanda aka tsare kananan yara masu zàngà-zàngà

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin fara bincike kan yanda aka tsare kananan yara masu zanga-zanga wanda aka gurfanar a kotu. A baya dai, an gurfanar da kananan yaran a kotu su 32 inda suka rika faduwa saboda tsananin yunwa, saidai shugaban 'yansandan ya bayyana cewa faduwar karyace kawai dan neman magane. Amma a sabuwar sanarwar da kakakin 'yansandan, Muyiwa Adejobi ya fitar yace shugaban 'yansandan yace a yi bincike dan gano ko an aikata ba daidai ba yayin tsaron yaran. Sannan ya sha Alwashin daukar mataki da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi yayin kamawa ko kula da yaran.
Hotunan Aurena Dake Ta Yawo A Kafafun Sadarwa An Yi Su Ne Bayan Daurin Aure, Kuma Bada Yawuna Aka Fitar Da Su Ba, Kuma Don Alah Ina Rokon Wadanda Suka Dora Da Su Goge, Cewar Abdulrahim Mansur Yelwa kalli bidiyi  jawabinsa

Hotunan Aurena Dake Ta Yawo A Kafafun Sadarwa An Yi Su Ne Bayan Daurin Aure, Kuma Bada Yawuna Aka Fitar Da Su Ba, Kuma Don Alah Ina Rokon Wadanda Suka Dora Da Su Goge, Cewar Abdulrahim Mansur Yelwa kalli bidiyi jawabinsa

Duk Labarai
Hotunan Aurena Dake Ta Yawo A Kafafun Sadarwa An Yi Su Ne Bayan Daurin Aure, Kuma Bada Yawuna Aka Fitar Da Su Ba, Kuma Don Alah Ina Rokon Wadanda Suka Dora Da Su Goge, Cewar Abdulrahim Mansur Yelwa. https://twitter.com/el_uthmaan/status/1853386068621512806?s=19 Abdulrahim Mansur Isa Yelwa ya magantu akan Hoton sa da Amaryasa dake yawo a Social Media tare da rokon duk wanda yayi posting ya goge.
Masu zanga-zanga sun nemi shugaban NNPCL ya sauka daga mukaminsa

Masu zanga-zanga sun nemi shugaban NNPCL ya sauka daga mukaminsa

Duk Labarai
A ranar Litinin an samu masu zanga-zanga da yaqa sun je Hedikwatar kamfanin mai na kasa,NNPCL inda suke nema shugaban kamfanin yayi murabus. Masu zanga-zangar wanda wasu kungiyoyin dake ikirarin kare hakkokin al'umma suka jagoranta sun zargi Shugaban na NNPCL, Abba kyari da rashin iya aiki saboda yanda man fetur ke ta kara tsada. Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar, Abdullahi Bilal ya bayyana cewa shugabancin kamfanin na NNPCL ya gaza. Masu zanga-zangar sun kuma nemi a dakatar da shigo da man fetur daga kasar waje inda suka ce yana lalatawa mutane motoci a Najeriya.
Kungiyar Likitocin Najeriya ta dakatar da aiki a jihar Kano saboda cin zarafin da kwamishiyar Jinkai, Amina Abdullahi Ganduje tawa wata Likita

Kungiyar Likitocin Najeriya ta dakatar da aiki a jihar Kano saboda cin zarafin da kwamishiyar Jinkai, Amina Abdullahi Ganduje tawa wata Likita

Duk Labarai
Kungiyar Likitocin Najeriya, NMA ta dakatar da aiki a Asibitin Murtala Muhammad dake Kano inda tace likitocin ta su daina aiki a asibitin. Kungiyar Likitocin ta dauki wannan mataki ne bayan cin zarafin da ta zargi kwamishiniyar jin kai ta jihar, Amina Abdullahi Ganduje da yiwa wata likita. Kungiyar tace tana neman gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya kori kwamishiniyar daga aiki kamin su koma bakin aiki. A sanarwar da ta fitar ta bakin shugabanta, Abdurrahman Ali kungiyar tace abin takaici ne lamarin da ya faru ranar 1 ga watan Nuwamba. Likitar na bakin aiki a bangaren kula da yara inda take kula da yara kusan 100 ita kadai, sai ga kwamishiyar ta shiga wajan inda ta rika cin zarafin likitar akan rashin wani magani da aka rubuta. Sanarwar kungiyar likitocin tace wannan kuma ba ...
Mu yarbawa ba zamu kara yadda wani ya zagi Tinubu ba saboda a wajan mu dan lelene>>Inji Doyin Okupe

Mu yarbawa ba zamu kara yadda wani ya zagi Tinubu ba saboda a wajan mu dan lelene>>Inji Doyin Okupe

Duk Labarai
Tsohon me magana da yawun shugaban kasa, Doyin Okupe ya bayyana cewa su yarbawa ba zasu kara yadda a rika zagin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba. Yace Tinubu dan lelene a wajansu. Ya bayyana hakane a hirar da gidan talabijin na Channels TV suka yi dashi. Saidai yace idan abubuwa a yanzu basa tafiya yanda ya kamata a yi hakuri nan gaba komai zai daidaita.
Daya daga cikin matan da mutuminnan na kasar Equatorial Guinea yayi lalata dasu kuma Bidiyon lalatar ya bayyana ta kàshè kanta

Daya daga cikin matan da mutuminnan na kasar Equatorial Guinea yayi lalata dasu kuma Bidiyon lalatar ya bayyana ta kàshè kanta

Duk Labarai
Labarin Shugaban hukumar binciken kudi ta kasar Equatorial Guinea Baltasar Engonga da ya rika lalata da matan manyan mutane kuma yana daukar Bidiyon lalatar ya dauki sabon salo. A jiya ne dai hutudole ya kawo muku labarin mutumin inda aka ruwaito cewa ya dauki bidiyo kusan 400 yana lalata da mata daban-daban. https://twitter.com/GucciStarboi/status/1853527395669606450?t=FX-xtQ8W58w1wTxj4KY06A&s=19 Tuni dai Bidiyon suka watsu sosai a kafafen sada zumunta. Daya daga cikin matan da yayi lalatar dasu da ta ga Bidiyon kuma surutu yayi yawa akan lamarin, ta kasa jurewa inda ta kashe kanta. Har yanzu da hukumomi na ci gaba da bincike akan lamarin.
Soyayyar Da Nake Yi Wa Tinubu Da Shettima Ta Sa An Je Har Wurin Sana’ata An Sace Min Turaren Da Nake Siyarwa, Don Haka Daga Yau Na Bar Tafiyar Tinubu/Shettima, Inji Bashir Musa Maiturare Daga Garin Nguru, Jihar Yobe

Soyayyar Da Nake Yi Wa Tinubu Da Shettima Ta Sa An Je Har Wurin Sana’ata An Sace Min Turaren Da Nake Siyarwa, Don Haka Daga Yau Na Bar Tafiyar Tinubu/Shettima, Inji Bashir Musa Maiturare Daga Garin Nguru, Jihar Yobe

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Soyayyar Da Nake Yi Wa Tinubu Da Shettima Ta Sa An Je Har Wurin Sana'ata An Sace Min Turaren Da Nake Siyarwa, Don Haka Daga Yau Na Bar Tafiyar Tinubu/Shettima, Inji Bashir Musa Maiturare Daga Garin Nguru, Jihar Yobe. Me za ku ce?
Ƴaƴana sun je karɓo kuɗin kai su asibiti aka kama su cikin masu zanga-zanga a Kano’

Ƴaƴana sun je karɓo kuɗin kai su asibiti aka kama su cikin masu zanga-zanga a Kano’

Duk Labarai
Ɗaya daga cikin iyayen yaran nan da gwamnatin Najeriya ta tuhuma da cin amanar ƙasa sakamakon zanga-zanga kan tsadar rayuwa ta ce ta yi farin ciki da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya ce a sake su. Fatima Muhammad ta ce 'ya'yanta biyu ne cikin yaran da aka kama lokacin da ta aike su karɓo kuɗin za a yi amfani da su wajen kai ɗaya daga cikinsu asibiti saboda ba shi da lafiya. "Wallahi farin cikin da muka ji ba zai musaltu ba," in ji Fatima. Shugabanni da kungiyoyi sun yi tir da kama yaran a wurin zanga-zangar da aka gudanar domin nuna fushi game da tsadar rayuwa daga 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024. Da yake jawabi a fadar shugaban ƙasa, Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce shugaban ƙasa ya ce a sake su duk inda suke a faɗin Najeriya, kuma a sadar da su ga iyayensu. ...
Za a fara rijistar baƙi a jihar Kano

Za a fara rijistar baƙi a jihar Kano

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kafa wani kwamitin ƙwararru da zai yi aikin yiwa baƙi ƴan ƙasashen waje mazauna birnin rijista musamman waɗanda suke gudanar da kasuwanci. Gwamnati ta ce ta ɗauki matakin ne domin samun alƙaluman mutanen da suka fito daga ƙasashen ƙetare kuma suke gudanar da harkokin kasuwanci a jihar, ta yadda za a haɓɓaka kudin shiga da kuma tsaro da samar da ayyukan yi. Kwamitin wanda ke ƙarƙashin ofishin sakataren gwamnatin Kano, zai tattara bayanan baƙi ƴan ƙasashen waje da ke aiki walau na kamfani ko a wata ma’aikata ko kuma kasuwanci. Shugaban kwamitin, Lawan Isa Kibiya ya ce aikin da za su yi zai taimaka wajen tabbatar da ganin baƙin waɗanda mafi yawa ƴan kasuwa ne su na biyan haraji kamar yadda doka ta yi tanadi. Ya ƙara da ...