Friday, December 19
Shadow
Nan da shekarar 2050 yawan ‘yan Najeriya zai karu kuma matsalar tsaro da hakan zai iya haifarwa yafi wanda ake ciki yanzu>>Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo yayi gargadi

Nan da shekarar 2050 yawan ‘yan Najeriya zai karu kuma matsalar tsaro da hakan zai iya haifarwa yafi wanda ake ciki yanzu>>Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo yayi gargadi

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, yawan 'yan Najeriya da ake da su zai iya karuwa zuwa Miliyan 400 nan da shekarar 2050. Obasanjo ya bayyana hakane yayin bude wani sabon gurin kimiyya da Fasaha a jihar Sokoto. Yace nan da shekaru 25 idan 'yan Najeriya suka karu suna bukatar aikin yi da abinci wanda idan basu samu ba, hakan zai iya kawo matsala. Yace hanya daya ce ta magance wannan matsala itace tun yanzu a baiwa matasa masu tasowa Ilimi. Yace idan kuwa ba haka ba, matsalar tsaron da za'a fuskanta nan gaba tafi wadda ake ciki yanzu.
Majalisar Shura za ta watsa zama da Sheikh Lawal Triumph kai tsaye

Majalisar Shura za ta watsa zama da Sheikh Lawal Triumph kai tsaye

Duk Labarai
Sakataren Majalisar Shura ta Kano, Shehu Wada Sagagi ya ce da farko za a fara da aike masa takardar gayyata tukunna wadda kuma za ta ƙunshi rana da lokacin da zai bayyana a gaban kwamitin. Ya kuma ƙara da cewa domin cire shakku daga zukatan al'umma an shirya yin zaman kai tsaye. "Wannan zama an shirya yin sa ne "Live" wato kai tsaye domin kowa ya ga irin tambayoyin da za a yi masa da kuma irin amsoshin da zai bayar," in ji Shehu Sagagi. Dangane kuma da labaran da ke yawo a kafafen watsa labarai kan cewa Majalisar ta dakatar da Malam Lawal Triumph daga yin wa'azi, sai Shehu Sagagi ya ce a'a ba wai an hana shi yin wa'azi ba ne kwata-kwata. "E an kawo shawara ne cewa wasu mutane suna ta fitintunu ana ta maganganu marasa daɗi har daga wajen jihar da ake ganin wannan abun zai iya ha...
Kalli Bidiyon: Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya dinka min kayan Alfarma har guda 30>>Inji Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami

Kalli Bidiyon: Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya dinka min kayan Alfarma har guda 30>>Inji Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa kaya na alfarma kala 30 Gwamnan jihar Borno wanda abokinsa ne ya dinka masa da sallah. Malam yace hadda rigar dake jikinsa na cikin kayan da Gwamnan ya dinka masa. Malam ya bayyana hakane a yayin da yake jan hankalo ga masu gori ga wadanda suka yiwa kyauta. https://www.tiktok.com/@sunnamedia/video/7554665274453118215?_t=ZS-90CFv7fFi9h&_r=1
Gwamnatin Jihar Legas ta baiwa matashiyarnan da ta so yin Alfasha da maza 100 amma daga baya tace ta tuba jakadiyar yaki da Miyagun Qayoyhi

Gwamnatin Jihar Legas ta baiwa matashiyarnan da ta so yin Alfasha da maza 100 amma daga baya tace ta tuba jakadiyar yaki da Miyagun Qayoyhi

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Lagos ta nada Mandy Kiss, Matashiyarnan data yi yunkurin shiga kundin Tarihin Duniya ta hanyar yin lalata da maza 100 jakadiyar yaki da miyagun kwayoyi. Lamarin ya baiwa mutane mamaki matuka lura da irin hanyar data dauka ta badala amma hukumomi suka bata aikin jakadanci. A baya dai, Hukumar hana sha da fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ta baiwa shahararren mawakinnan kuma mashayi, Naira Marley jakadan yaki da ta'ammuli da miyagun Kwayoyi. Da take martani kan wannan jakadanci data samu, Tace a baya da take magana a matsayin mutuniyar kirki babu wanda ya kulata amma yanzu da ta dau hanyar badala gashi har ta zama jakadiya.
Shugaban bankin Access Bank ya sayi gidan Dala Miliyan $20 a Landan

Shugaban bankin Access Bank ya sayi gidan Dala Miliyan $20 a Landan

Duk Labarai
Shugaban bankin Access Bank, Roosevelt Ogbonna ya sayi gidan dala Miliyan $20 a Landan. !Ya sayi gidanne a unguwar masu kudi da ake cewa, Billionaires’ Row kamar yanda kafar Bloomberg ta ruwaito. Rahotan yace da farko kudin gidan sun fi haka amma daga baya aka masa sauki ya kuma saya. Wannan gida da ya siya yana daga cikin ciniki masu tsada da aka yi a Landan wanda ya dauki hankula.
‘Yan darika Taron Yuyu ne, Duk Kano, babu Majalisin da ya kai na Gadon kaya cika, Dan haka Me Girma Gwamnan Kano kada ka yadda su ce maka bamu da yawa>>Inji Malam Kan neman da ake Gwamnatin Kano ta dauki mataki kan Malam Lawal Triumph

Malam yace ba gaskiya bane Abinda ake gayawa Gwamnan Kano cewa 'yan Izala basu da yawa a jihar. Yace sun sha hawa mumbari suna neman a baiwa Gwamna Abba Kujerarsa saboda shine yaci zabe. Yace kuma duk Kano babu majalisin dake cika kamar na gadon Kaya. Dan haka ya yi kira ga gwamna cewa, ya sa ma ransa mulki Allah ne ke bayarwa. https://www.tiktok.com/@ali_d_abba/video/7555267558375492886?_t=ZS-90BvDpfxs0X&_r=1
Kalli Bidiyo: Idan dai kai Kirista ne na gaskiya, Bai kamata a ganka da Guru ko laya ba, sannan bai kamata kana zuwa gurin Boka ba>>Inji Wannan Faston

Kalli Bidiyo: Idan dai kai Kirista ne na gaskiya, Bai kamata a ganka da Guru ko laya ba, sannan bai kamata kana zuwa gurin Boka ba>>Inji Wannan Faston

Duk Labarai
Wannan Wani Fasto ne da ya dauki hankula sosai bayan da yayi wa'azin cewa Kirista na Gari baya zuwa wajan Boka ko daura laya ko Guru. Wasu sun rika ce masa Fasto dan Izala inda wasu suka rika ce masa, Allah yasa ya musulunta. https://www.tiktok.com/@ndbcvihausa/video/7555449846900116743?_t=ZS-90BuSukkwiH&_r=1
Kalli Bidiyon yanda Hassan Make-Up ya kama Otal din Miliyan 3 da rabi a Makkah inda yaje aikin Umrah

Kalli Bidiyon yanda Hassan Make-Up ya kama Otal din Miliyan 3 da rabi a Makkah inda yaje aikin Umrah

Duk Labarai
Tauraron Tiktok Hassan Make-Up yana kasar Saudiyya inda yake aikin Umrah. An ga yanda ya kamata otal dake kusa da dakin Ka'aba wanda aka bayyana da cewa ana biyan Naira Miliyan 3.5 kudin Najeriya. Wata kawarsa data kai masa ziyara ce ta bayyana hakan. https://www.tiktok.com/@fanneshuwa15/video/7555282877152283922?_t=ZS-90BtjuQylBh&_r=1
Da Duminsa: Gwamnatin Jihar Kano ta dauki mataki akan Malam Lawal Triumph, saidai bai yiwa dalibansa dadi ba

Da Duminsa: Gwamnatin Jihar Kano ta dauki mataki akan Malam Lawal Triumph, saidai bai yiwa dalibansa dadi ba

Duk Labarai
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa'azi Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa ta sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa'azi. A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a yau Laraba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar ya kare kan sa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Ma'aiki. A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakin sa a matakin Majalisar ta shura. Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya bukaci da a kyale kwamitin ya kammala aikin sa. Sagagi ya tabbatar da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da son rai ko rashin adalci ba...
Kalli Bidiyo:Jama’ar Katsina ku yi Hakuri, kamin in hau mulki na yi Alkawarin duk wata zan rika bada bayanin yawan kudaden da muka samu da yawan wanda muka kashe, amma yanzu da na zama Gwamnan naga abin ba zai yiyu ba>>Inji Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya baiwa al'ummar Jihar Hakuri inda yace kamin ya hau mulki yayi Alkawarin rika bayar da ba'asi kan yawan kudaden da aka samu da wanda aka kashe. Yace amma bayan da ya hau yaga abin ba mai yiyuwa bane. Gwamnan yace dalili kuwa shine Wasu kudaden idan aka karbosu kudin aikin gwamnatin data wucene za'a biya, hakanan wasu kudaden kuma aikin da aka yi shekarar data wucene za'a biya dasu. A karshe dai yace shima dan Adam ne dan haka yana neman Afuwa. Kalli Bidiyon jawabinsa a kasa; https://www.tiktok.com/@mps_mediang/video/7553746884012035346?_t=ZS-90BqPMn9FZ3&_r=1