A karo na 2, Sanata Godswill Akpabio karara ya bayyana tsoron Trump yake ji yayin da ‘yan Najeriya suka bukaci jin Abinda majalisar Dattijai zata ce kan Barhazhanar da Trump din yawa Najeriya
Rahotanni sun bayyana cewa an samu wata sa in sa tsakanin Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da mataimakinsa, Sanata Jibrin Barau.
A na daf da gama zaman majalisar na ranar Talata ne sai Akpabio yace 'yan Najeriya da yawa sun mika musu bukatar jin abinda zasu ce kan barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump yawa Najeriya.
Saidai yace wanene shi, bai isa ya baiwa Trump Amsa ba, suna jiran abinda duk Gwamnatin tarayya tace akan lamarin haka za'a yi.
Saidai Sanata Barau Jibrin ya mike yacewa Akpabio ka daina jin tsoron Trump kai ne mutum na 3 mafi mukami a Najeriya kasa me cin gashin Kanta.
Barau yace Trump makaryaci ne kuma yawa Najeriya karyar cewa ana yiwa kiristoci kisan kiyashi kuma ya kamata a gaya masa ba gaskiya bane abinda ya fada.
Saidai Akpab...








