Friday, June 26
Shadow

Duk Labarai

Zamu fara amfani da Tattalin Arzikin Halal wanda kayan amfanin da Addinin Musulunci kadai ya yadda ayi kasuwancinsu zamu rika cinikinsu>>Inji Gwamnatin Shugaba Tinubu

Zamu fara amfani da Tattalin Arzikin Halal wanda kayan amfanin da Addinin Musulunci kadai ya yadda ayi kasuwancinsu zamu rika cinikinsu>>Inji Gwamnatin Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, zata fara amfani da tattalin arziki na halal, wanda a Turance ake cewa Halal Economy Wannan tattalin arziki ana kasuwancin kayan amfanin da addinin musulunci kadai ya yadda ayi amfani dasu ne, misali idan aka zo wajan nama, ba za'a yi kasuwancin Naman Alade ba da sauransu. Mataimakin shugaban ma'ikatan fadar shugaban kasa, Senator Ibrahim Hassan Hadejia ne ya bayyanawa manema labarai na Thisday haka. Yace kasancewar Najeriya na amfani da irin wadannan kaya suka ga cewa ya kamata suma su shiga harkar wannan tattalin arziki da ake yayi suma ayi dasu. Yace kuma kar wani yayi tunanin wai saboda addini ne, yace Halal Economy ya na kusa da kaiwa darajar Dala Tiriliyan 7. Yace kuma a cikin kasashen da suke amfani dashi, ka...
Kalli Albashin da Sojojin Najeriya ke karba da wanda sojojin kasar Ghana dana Afrika ta kudu ke karba

Kalli Albashin da Sojojin Najeriya ke karba da wanda sojojin kasar Ghana dana Afrika ta kudu ke karba

Duk Labarai
A cikin kwanakin da mukene wani Soja ya fito yake kokawa kan kalar abincin da ake basu wanda bashi da yawa bashi da inganci. An ga abincin karamin Bokitin Fenti na shinkafa da Karamin Bokitin Fenti na wake da Manja lita guda da sauransu irin su magi haka da sauransu. Hakan ne yasa wasu masu bincike suka nemo Albashin da ake biyan sojojin kasar Ghana dana kasar Afrika ta kudu inda suka kwatantashi dana sojojin Najeriya. Ga albashin kamar haka: Nigeria — ₦104,000 (~$64)Ghana — GHS 1,000–1,500 (₦157,000 – ₦235,000)South Africa — R8,000–R12,000 (₦704,000 – ₦1.06 Million)
Wata Sabuwa: Za’a kara kudin kiran waya da na aika sakon waya a Najeriya>>NCC

Wata Sabuwa: Za’a kara kudin kiran waya da na aika sakon waya a Najeriya>>NCC

Duk Labarai
Hukumar kula da harkar Sadarwa ta kasa, NCC ta bayyana fara duba farashin kiran waya dana aikawa da sako a Najeriya. Hakan zai sa a kara kudin kiran dana sako kamar yanda Rahotanni suka nunar. Wani me ruwa da tsaki a harkar sadarwar, Wole Adenekan ya tabbatar da hakan inda yace karin ya zama dole saboda an samu sauye-sauyen tattalin arziki da na kimiyya da fasaha. Yace maimakon a rika biyan kudi kadan amma ba'a samun sabis me kyau, gara a rika biyan ainahin kudin kiran dana aika sako sabis din ya inganta. Hakan na zuwane a yayin da 'yan Najeriya da dama ke kokawa da matsalar tsaro.
Tinubu ya gaya mana cewa ba zai goyi bayan zaben gaskiya ba, wanda ya ga dama yayi zabe wanda bai ga dama ba kar yayi>>Inji Dan takarar jam’iyyar SDP Adewole Adebayo

Tinubu ya gaya mana cewa ba zai goyi bayan zaben gaskiya ba, wanda ya ga dama yayi zabe wanda bai ga dama ba kar yayi>>Inji Dan takarar jam’iyyar SDP Adewole Adebayo

Duk Labarai
Dan takarar shugaban jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo ya zargi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da cewa yace ba zai goyi bayan zaben gaskiya ba. Adewole yace sun je sun samu shugaban kasar ne kan yanda za'a gyara harkar zabe amma ya gaya musu cewa shima lokacin yana da adawa ya sha wuya sannan kuma zabe iyawane, wanda ya iya Allonsa ya wanke. Ya bayyana cewa, shugaban kasar ya gaya musu cewa suna bata masa rai. Adewole yace a daidai wannan lokacin ya daina kallon Tinubu a matsayin shugaban kasa inda yake kallonsa kamar kowane dan siyasa. https://twitter.com/i/status/2067379198004531482
Kalli Yanda aka kama wani mutum dake ajiye kashin mutane Buhu-Buhu a gidansa dake Kano, duk ya addabi Makwabta da wari

Kalli Yanda aka kama wani mutum dake ajiye kashin mutane Buhu-Buhu a gidansa dake Kano, duk ya addabi Makwabta da wari

Duk Labarai
Hukumomi a Kano sun kama wani mutum me suna Mohammed Saidu saboda tara kashin mutane buhu-buhu a kofar gidansa. Hakan yasa wari ya damu mutanen unguwar inda aka yi ta kokarin yin magana dashi dan ya daina amma yaki. Hakane yasa makwabtansa suka kai maganar zuwa kotu. Mai Shari'a Halima Wali ta kotun Magistrate ta yanke masa hukuncin daurin kwanaki 14 a gidan yari da kuma tarar Naira 100,000. A yayin zaman kotun dai Muhammad Saidu wanda sana'ar kwashe kashi yake yace yana tarawa ne yana sayarwa da manoma inda ya amsa zargin da ake masa. Kotu ta bashi umarnin dauke kashin daga kofar gidansa sannan yayi alkawarin ba zai sake tarawa ba.
Bayan kammala wasannin zagayen farko na World Cup duba kuga yanda Groups suke

Bayan kammala wasannin zagayen farko na World Cup duba kuga yanda Groups suke

Duk Labarai
Wannan jadawalin yanda kowace kasa take a group dintane na gasar cin kofin Duniya, World Cup dake gudana a kasar Amurka bayan kammala zagayen farko. GROUP A1. Mexico - 3 Points (+2)2. South Korea - 3 Points (+1)3. Czech Republic - 0 Points (-1)4. South Africa - 0 Points (-2)Mexico lead the group on goal difference, while South Africa have work to do after a disappointing start. GROUP B1. Switzerland - 1 Point2. Canada - 1 Point3. Qatar - 1 Point4. Bosnia and Herzegovina - 1 PointThe most balanced group so far. Everyone is level on points and goal difference. GROUP C1. Scotland - 3 Points (+1)2. Morocco - 1 Point3. Brazil - 1 Point4. Haiti - 0 Points (-1)Scotland are the surprise leaders after Matchday 1. GROUP D1. United States - 3 Points (+3)2. Australia - 3 Points (+2)3. Turk...

Kalli Bidiyon: A karshe dai bayan da mutane da yawa keta kokarin a kulle masa YouTube channel, Tauraron fina-finan Hausa, Lawal Ahmad ya fito ya bayar da hakuri kan zage-zagen da yayi

Duk Labarai
Bayan da ake ta yunkurin kulle masa YouTube channel dinsa na Bakori TV ta hanyar yin reporting din channel din. Tauraron fina-finan Hausa, Lawal Ahmad ya fito ya bayar da hakuri kan kalamansa da zage-zagen da yayi. Lawal Ahmad yace bacin raine yasashi hakan kuma jama'a da yawa sun san cewa ba halinsa bane. https://www.tiktok.com/@mshareefinborno/video/7652462800983379208?_r=1&_t=ZS-97JI00k8upj
Kalli Bidiyon: Duk abubuwan da ake fada ko zagin da Davido yawa mijina basu dameni ba, abinda naji dadinshi shine sakon ya kai wajan Davido>>Inji Matar Rarara A’ishatulhumaira

Kalli Bidiyon: Duk abubuwan da ake fada ko zagin da Davido yawa mijina basu dameni ba, abinda naji dadinshi shine sakon ya kai wajan Davido>>Inji Matar Rarara A’ishatulhumaira

Duk Labarai
Matar Tauraron mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, A'ishatulhumaira ta bayyana jin dadinta game da martanin da Davido yawa mijinta. Tace duk wani abu daga bayane babban abinda taji dadi shine da sakon Mijin nata ya kai kunnen Davido. Tace kuma game da maganar yaren Turanci, dama can mijinta mawakin Hausane, kuma bai ce yana jin yaren Tauranci ba. Tace dan baya jin yaren Turanci ba aibu bane. https://www.tiktok.com/@boshonishadi6/video/7652531880746683664?_r=1&_t=ZS-97JEj7kjmxc