Sunday, April 19
Shadow

Duk Labarai

Da Duminsa:Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana a kotu a yau sanye da tutar jam’iyyar ADC

Da Duminsa:Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana a kotu a yau sanye da tutar jam’iyyar ADC

Duk Labarai
A yau, Laraba, Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana a gaban babbar kotun tarayya dake Kaduna inda kotun zata saurari bukatarsa ta neman beli. Wani abu da ya dauki hankula shine ganin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da hatimin jam'iyyar ADC a jikin rigarsa. An baza jami'an tsaro a farfajiyar Kotun inda aka hana zirga-zirga a wajan. Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na fuskantar tuhume-tuhumen aikata ba daidai ba a ofishinsa da kuma almundahanar kudade.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na ta shan yabo saboda irin kulawar da ya baiwa Mahaifiyarsa lokacin tana raye, ko da yana Gwamna yana bata lokaci sosai

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na ta shan yabo saboda irin kulawar da ya baiwa Mahaifiyarsa lokacin tana raye, ko da yana Gwamna yana bata lokaci sosai

Duk Labarai
Jama'a da yawa a kafafen sada zumunta sai yabon Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai suke yi saboda irin kulawar da ya baiwa mahaifiyarsa lokacin tana raye. Ko da yana Gwamna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya rika baiwa Mahaifiyarsa Lokaci sosai yana bata kulawa. Wani Bidiyo da aka gani na mahaifiyar Nasiru tana yaba masa tana masa kirari ya karade kafafen sada zumunta sosai. https://twitter.com/i/status/2039049027904266607
Rahotanni naa cewa akwai yiyuwar Rarara zai bar jam’iyyar APC zuwa ADC

Rahotanni naa cewa akwai yiyuwar Rarara zai bar jam’iyyar APC zuwa ADC

Duk Labarai
Wasu rahotanni dake yawo a kafafen sada zumunta sun bayyana cewa Tauraron mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara na shirin barin jam'iyyar APC zuwa ADC. Rahoton yace abinda ya batawa Rarara rai har yake shirin barin jam'iyyar ta ADC shine rashin tafiyar da ba'a yi dashi ba zuwa kasar Ingila da shugaba Tinubu ya kai ziyara. An dai hangi mawakiyar kudu, Tiwa Savage a cikin tawagar shugaba Tinubu a ziyarar da ya kai Ingilar inda aka rika cece-kuce cewa ba a dauki mawakin Arewa ko guda a cikin tafiyar ba. Zuwa yanzu dai babu abinda Rarara yace akan lamarin. https://twitter.com/i/status/2039102682473124306
ICPC ta sake kama Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bayan zaman kotun yau

ICPC ta sake kama Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bayan zaman kotun yau

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar ICPC ta sake kama tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a yau bayan zaman kotun da aka yi. Malam Nasiru Ahmad El-Rufai dai ya nemi beli inda kotu ta saka ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu dan yanke hukunci. A baya dai ICPC sun ce sun saki malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne saboda tausayi bayan rasuwar mahaifiyarsa inda ya samu halartar jana'izar da aka mata. https://twitter.com/i/status/2038967971477962970
Da Duminsa:  Rahotanni na cewa, wasu matasa sun yiwa Musa Mai Sana’a na jaki

Da Duminsa: Rahotanni na cewa, wasu matasa sun yiwa Musa Mai Sana’a na jaki

Duk Labarai
Rahotanni na ta yawo a kafafen sada zumunta inda ake yada cewa wasu matasa sun tare Tauraron fina-finan Hausa, Musa Mai Sana'a inda suka masa na jaki. Shafin @kafinhausa dake X ya wallafa cewa, lamarin ya farune a Sharada dake Kano. Mai Sana'a dai bai tabbatar da hakan da kansa ba, sannan babu wata kafa data kawo labarin, saidai labarin ya dauki hankula a kafafen sada zumunta inda mutane ke ta bayyana ra'ayoyinsu akai. https://twitter.com/i/status/2038737606788149299

Da Duminsa: Bayanin Halin da ake ciki a kotun da aka mayar da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a yau

Duk Labarai
A yaune dai ICPC ta mayar da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai babbar kotun jihar inda ake masa shari'a game da zargin Almundahanar kudade. Saidai kotun tace zaman kotun ba zai yiyu ba saboda dayan wanda ake musu shari'ar tare da malam Nasiru Ahmad El-Rufai bai zo ba saboda bai da lafiya kuma shari'ar ta mutum biyu ce dan haka ba zai yiyu a ci gaba da ita ba sai yana nan. A yanzu za'a tafi da malam Nasiru Ahmad El-Rufai zuwa babbar kotun tarayya inda za'a saurari neman belin da yayi. KARIN BAYANI: An kuma je babbar kotun tarayya inda El-Rufai ya shigar da korafin neman beli, saidai an daga ci gaba da sauraren karar har sai nan da 1 ga watan Afrilu
Dubban Mutane sun kamu da cutar Kanjamau daga wajan Janairu na shekarar 2026 zuwa yanzu

Dubban Mutane sun kamu da cutar Kanjamau daga wajan Janairu na shekarar 2026 zuwa yanzu

Duk Labarai
Sabbin alkaluma sun nuna cewa, dubban mutanene suka kamu da cuta me karya garkuwar jiki, wadda aka fi sani da Kanjamau a Najeriya. An fitar da yawan mutanen da suka kami a kowace jiha, yayin da a Arewa, Jihar Kaduna ce kan gama da yawan mutane 800 da suka kami da cutar. Yayin da jihar Yobe itace ta karshe inda mutane 100 ne kacal auka kamu da cutar a wannan tsakani. Numbers of newly tested HIV positive patients in Nigeria (Jan-Mar, 2026) Lagos: 2,298 ⁠Benue: 1,949 ⁠Akwa Ibom: 1,159 ⁠Rivers: 1,137 ⁠Anambra: 1,013 ⁠Kaduna: 842 ⁠Delta: 803 ⁠Oyo: 763 ⁠Ogun: 751 ⁠Plateau: 662 ⁠Imo: 640 ⁠Nasarawa: 615 ⁠Taraba: 605 ⁠FCT: 579 ⁠Abia: 527 ⁠Edo: 512 ⁠Enugu: 479 ⁠Kano: 476 ⁠Kogi: 422 ⁠Cross River: 396 ⁠Niger: 387 ⁠Adamawa: 38...
Ashe Tsugune bata kare ba, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai  ya bayyana wata Mugunta da Gwamnati ta shirya masa dan tursasashi ya amince da bukatun Gwamnatin

Ashe Tsugune bata kare ba, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana wata Mugunta da Gwamnati ta shirya masa dan tursasashi ya amince da bukatun Gwamnatin

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi zargin cewa, Gwamnati na son kama yayansa, Bashir El-Rufai dan a tursasashi ya amince da bukatun Gwamnatin. Yace dalili ma kenan da yasa suka ce babban yayan nasu ya tsaya a birnin Cairo na kasar Egypt kada ya dawo Najeriya dan kar a kamashi. Yace yanzu haka yana can. ElRufai ya bayyana hakane a wajan zaman makokin mahaifiyar sa data rasu inda yakewa mutane godiya da irin aoyayyar da suka nuna musu. https://twitter.com/i/status/2038828878110626286
Farashin dala a kasuwar Chanji ayau, Talata

Farashin dala a kasuwar Chanji ayau, Talata

Duk Labarai
Farashin Dala a kasuwar chanji ta Gwamnati a yau Talata, 31 ga watan Maris na shekarar 2026 ya farane akan Naira ₦1,385.60 kowace dala. Saidai da gari ya kara wayewa, farashin ya sauka zuwa Naira ₦1,383.37 akan kowace dala. A kasuwar bayan fage ta Legas da Abuja kuwa farashin dalar yana akan naira ₦1,405 zuwa Naira ₦1,420 akan kowace dala daya.