Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ya ziyarci jihar Sokoto game da Làkùràwà
Mai riƙon muƙamin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftana Janar Olufemi Oluyede ya nemi da a haɗakai domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar yankin arewa maso yamma.
Janar Oluyede ya yi kiran ne a lokacin da ya kai ziyararsa ta farko a jihar Sokoto a jiya Lahadi, inda ya ziyarci sansanin dakarun da ke Tangaza da Illela.
A kwanakin nan ne aka samu ɓullar wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ta addabi yankin jihar Sokoto da Kebbi, wadda ake wa laƙabi da Lakurawa, da aka ce ta fito ne daga yankin Sahel.
A ranar Juma'a al'ummar garin Mera da ke ƙaramar hukumar Augie ta jihar Kebbi suka rasa mutum aƙalla 15 a wani artabu da suka yi da mayaƙan ƙungiyar ta Lakurawa.
Yayin da ya ziyarci sansanonin Janar Oluyed, ya yaba wa sojojin tare da ba su tabbacin samun cikakken goyo...