Da Duminsa: Rahotanni sun bayyana cewa, Fusatattun Matasa sun Bankawa gidan Nafiu Bala Gombe dake ikirarin shine shugaban ADC wta, saidai ‘yansanda sun yi magana kan lamarin
Wasu Rahotanni sun rika yawo cewa, Fusatattun matasa sun bankawa gidan Nafiu Bala Gombe dake ikirarin cewa, shi ne shugaban jam'iyyar ADC wta.
An ga Hotunan na yawo a kafafen sada zumunta inda wani gida ke ci da wta wanda wasu ke cewa gidan Nafiu Bala Gombe dinne a jihar Gombe
Saidai hukumar 'yansandan jihar ta bakin me magana da yawunta, DSP Buhari Abdullahi ta bayyana cewa rahoton ba gaskiya bane.








