Gwamna Dauda Lawal Dare ya baiwa Shugaba Tinubu sharadin sauke Matawalle daga karamin Ministan tsaro kamin ya koma APC
Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa, Gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sharadin sauke Matawalle daga Ministan tsaro kamin ya yadda ya koma jam'iyyar APC.
Jaridar Sunnews ta bayyana cewa, a baya gwamnan ya zauna da shugaban kasa Tinubu a Paris tare da gwamnonin Taraba da Enugu inda ya bayyana aniyarsa ta komawa APC.
A yanzu da Muhammad Badaru Abubakar ya sauka daga ministan tsaro, Gwamna Dauda ya sake dawowa da bukatarsa inda yace a sauke Matawalle daga karamin Ministan tsaro shi kuma zai koma APC.
Yayi Alwashin jawo mutane da yawa mabiyansa zuwa jam'iyyar ta APC a jihar Zamfara.








