Monday, December 15
Shadow
Idan kuka sake kuka kkasheni zaku dandana kudarku>>Trum ya gayawa Iran

Idan kuka sake kuka kkasheni zaku dandana kudarku>>Trum ya gayawa Iran

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gargadi kasar Iran da cewa idan suka sake suka kasheshi zasu dandana kudarsu. A baya dai lokacin Trump yana yakin neman zabe an kaiwa Trump hari inda aka so kasheshi saidai ya tsallake rijiya da baya inda kuma aka zargi cewa kasar Iran ce ta kai masa harin. Saidai tuni kasar Iran ta fito ta karyata wannan zargin da ake mata inda tace ba itace ta kaiwa Trump hari ba. Wasu masu sharhi kan al'amuran yau da kullun sun bayyana cewa, watakila kasar ta Amurka na wannan maganane saboda kawai tana son fara yakin kai tsaye da kasar Iran.
Innalil-Lahi wa’inna iLaihi rajiun: Allah ya yiwa dalibai almajirai (17) Rasuwa Agarin Kauran-Namoda sanadiyyar Gobara wadda ta shafe awa uku tana ci

Innalil-Lahi wa’inna iLaihi rajiun: Allah ya yiwa dalibai almajirai (17) Rasuwa Agarin Kauran-Namoda sanadiyyar Gobara wadda ta shafe awa uku tana ci

Duk Labarai
Innalillahi wa Inna Ilaihi rajiun ibtila'in gobarar wuta yayi sanadiyyar mutuwar almajirai fiyeda 15 tareda jikkata wasu a daren jiya makantar malan ghali bakin kasuwa dake Kauran Namoda Jihar Zamfara. Rahotanni da muke samu shine wutar ta auku ne a daren ranar Talata kuma Almajirai da yawa sun jikkata. Hasbunallahu wa ni'imatil wakell.Ubangiji Allah shi gafarmasu ya bamu iKon cinye Wannan jarabawa.
Trump yace Fàlàsdìnàwà su fice daga Gaza saboda America nason kwace Gazar da sake yi mata ginin zamani

Trump yace Fàlàsdìnàwà su fice daga Gaza saboda America nason kwace Gazar da sake yi mata ginin zamani

Duk Labarai
Donald Trump ya firgita Falasɗinawa kan shawarwarinsa game da makomar zirin Gaza, saboda ya ce Amurka za ta ƙwace iko da zirin tare sauya fasalinsa. Wannan ne sauyi mafi girma game da manufofin Amurka kan yankin gabas ta tsakiya cikin gomman shekaru. Trump ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a fadar White House tare da firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. "Amurka za ta ƙarbi ikon zirin Gaza kuma za mu mallake zirin kuma mu dauki alhalin kwance nakiyoyin da aka dąsa sannan kuma gyara wuraren da aka lalata," in ji Trump. Nan da nan firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya nuna jin dadinsa ga kalaman na Mr Trump, inda ya ce hakan zai canza tarihi. Netanyahu ya ce "ina kara maimaitawa, muradinmu uku ne kuma na uku shi ne tabbatar da cewa zirin Gaza bai kara za...
Karya kika min, ban taba cewa, Tinubu Barawo ba>>Nuhu Rubadu ya gayawa Naja’atu Muhammad inda yace ta tabbatar ta fito ta bashi Hakuri nan da kwanaki 7

Karya kika min, ban taba cewa, Tinubu Barawo ba>>Nuhu Rubadu ya gayawa Naja’atu Muhammad inda yace ta tabbatar ta fito ta bashi Hakuri nan da kwanaki 7

Duk Labarai
Me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar Tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa, Maganar da Naja'atu Muhammad ta yi akan cewa ya taba cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu barawo ba gaskiya bane. Bidiyon da ya watsu a Tiktok ya dauki hankula sosai inda akai ta martani kala-kala. Naja'atu Muhammad ta bayyana cewa, Nuhu Ribadu ya yi wannan magana ne a lokacin yana shugaban hukumar EFCC. Saidai lauyan Nuhu Ribadu, Dr Ahmed Raji, SAN ya bayyana cewa maganar Naja'atu ba gaskiya bane kuma suna neman nan da kwana 7 ta fito ta bayar da hakuri. Sun ce idan bata yi hakan ba, basu da zabi da ya wuce su kaita kotu.
Matashiya ta kafa tarihin kasancewa wadda tafi kow dadewa rungume da bishiya a Duniya

Matashiya ta kafa tarihin kasancewa wadda tafi kow dadewa rungume da bishiya a Duniya

Duk Labarai
Wata matashiya daga kasar Kenya ta kafa tarihin kasancewa wadda tafi kowa dadewa rungume da bishiya a Duniya, wannan bajinta tata tasa aka sakata cikin Kundin Tarihin Duniya. Matashiyar me suna Truphena Muthoni 'yar Kimanin shekaru 21 'yar Gwagwarmaya ce ta muhalli. Ta yi wannan bajintace a wajan shakatawa dake Michuki Park a Birnin Nairobi na kasar ta Kenya. Wakilin majalisar Dinkin Duniya bangaren Muhalli a kasar Kenya, Ababu Namwamba ya jinjinawa matashiyar kan wannan bajinta da ta yi. https://www.youtube.com/watch?v=F-3RhMd1aSk?si=c5FwHw6cKHU-IXI-
Wata Sabuwa, an shigar da karar neman tsige shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu daga kan kujerarsa saboda cin zalin ‘yan kasa

Wata Sabuwa, an shigar da karar neman tsige shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu daga kan kujerarsa saboda cin zalin ‘yan kasa

Duk Labarai
Wani lauya me rajin kare hakkin al'umma, Mr. Olukoya Ogungbeje ya kai karar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda yace ya take hakkin 'yan kasa. Ya kai karar Tinubu ne babbar kotun tarayya dake Abuja inda yace Tinubun yana take hakkin 'yan kasa da murkushesu a duk sanda suka yi yunkurin nuna rashin jin dadin mulkinsa ta hanyar zanga-zanga. Ya kawo musalin Zanga-zangar da aka yi a watan Agusta na shekarar data gabata inda yace Gwamnatin Tinubu ta murkushe masu zanga-zangar da take hakkinsu na 'yan kasa. A cikin wadanda yake karar hadda babban lauyan Gwamati kuma Ministan shari'a, Prince Lateef Fagbemi inda yace yana neman kotu ta baiwa majalisar tarayya umarnin fara shirin tsigesu duka daga mukamansu saboda laifukan da suka aikata sun bada damar a tsigesu. Saidai lauyan Shugaban...
Kamar dai yanda suka rika fadi akan Tallafin Man Fetur, Gwamnatin tarayya tace wasu kalilanne ke amfana da tallafin wutar lantarki

Kamar dai yanda suka rika fadi akan Tallafin Man Fetur, Gwamnatin tarayya tace wasu kalilanne ke amfana da tallafin wutar lantarki

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana biyan Naira Biliyan 200 a matsayin tallafin wutar lantarki duk wata. Kuma tace wasu kalilanne da basu wuce kaso 25 cikin 100 na al'umma ba ke amfana da wananna tallafi inda tace talafin baya kaiwa ga wadanda ya kamata. Babbar me baiwa shugaban kasa shawara akan makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan a ranar Litinin. Ta yi maganane akan rahoton dake cewa za'a kara farashin wutar lantarki da kaso 65 cikin 100. Tace maganar da tayi ba'a fahimceta ba, tace abinda ta fada shine kudaden da 'yan Najeriya ke biya na wutar lantarki suna biyan kaso 65 cikin 100 ne inda gwamnati ke biya musu sauran. Tace amma mafi yawa, masu kudi ne kalilan suka fi amfana da wannan tallafi na wutar lantarkin. Game da karin kudin wuta da kuma zargin cewa ...
Babu maganar tattaunawa, ba zamu rage ko sisi a karin kudin kiran da muka yi ba>>Kamfanonin Sadarwa Irin su MTN, Airtel suka bayyana

Babu maganar tattaunawa, ba zamu rage ko sisi a karin kudin kiran da muka yi ba>>Kamfanonin Sadarwa Irin su MTN, Airtel suka bayyana

Duk Labarai
Kungiyar kamfanonin sadarwa ta bayyana cewa babu wani abu da zai sa su rage karin farashin kudin kiran waya da kaso 50 da gwamnati ta amince musu. Kamfanonin sun nemi yin karin kaso 100 bisa 100 amma hukumar sadarwa ta NCC ta amince musu da yin karin kaso 50 cikin 100. Wannan karin ne yasa kungiyoyin fafutuka suka ce basu amince dashi ba dan zai saka mutane a cikin wahala. Saidai shugaban kungiyar masu kamfanonin sadarwa ta Najeriya Gbenga Adebayo yace ba zasu rage ko sisi a cikin kaso 50 din da suka kara ba. Yace ragin zai zama kamar mutum ne dake bukatar numfashi amma a ki bashi, yace muddin ana son ci gaba da samun sabis me karfi da dorewa da kuma kara fadada ayyukansu to sai an bari an yi wannan kari.
Da Duminsa: Kungiyar kwadago ta NLC ta fasa zanga-zanga kan karin kudin kiran waya

Da Duminsa: Kungiyar kwadago ta NLC ta fasa zanga-zanga kan karin kudin kiran waya

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta NLC ta fasa yin zanga-zanga data shirya kan karin kudin kiran waya da kaso 50. A ranar Talata ne dai Kungiyoyin na kwadago da sauran na fafutuka suka shirya zanga-zanga dan nuna adawa da wannan kari. kungiyoyin sun bayyana dakatar da zanga-zangar ne bayan ganawa da wakilan Gwamnatin tarayya a ranar Litinin a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya a Abuja. Shugaban kungiyar kwadagon Joe Ajaero yace sun dakatar da zanga-zangar ta yaune saboda gwamnati ta amince ta kafa kwamiti na musamman da zai duba kowane bangare dan samar da mafita akan lamarin.
Da Duminsa:Shugaba Tinubu ya amince da kafa jami’ar Kimiyyar Muhalli a Ogoni jihar Rivers

Da Duminsa:Shugaba Tinubu ya amince da kafa jami’ar Kimiyyar Muhalli a Ogoni jihar Rivers

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa kudirin dokar kafa jami'ar kimiyyar Muhalli a Ogoni dake jihar Rivers, Niger Delta. Shugaban ya sakawa dokar hannu ne a fadarsa dake Abuja da yammacin ranar Litinin. Shugaban yace wannan babbar nasara ce a kokarin Najeriya wajan kawo ci gaban muhalli, Ilimi, da ci gaba me dorewa. Yace wannan jami'a na nuni da cewa gwamnati ta damu da ci gaban al'ummar yankin gaba daya inda yace shekaru da yawa mutanen yankin na ta fafutukar ganin sun samawa kansu mafita ta bangaren gyaran muhalli. Shugaban ya kuma jinjinawa majalisar tarayya bisa kokarin amincewa da wannan kudirin dokar. Ya kuma jawo hankalin masu ruwa da tsaki da suka hada da matasa, iyaye, da masu zaman kansu da su goyawa wannan jami'a baya.