Tauraron fina-finan Hausa, Garzali Miko ya bayyana a wani Bidiyo yana daukar sauran abinci daga kwanukan mutane yana ci a wajan Biki.
Lamarin ya dauki hankula inda akai ta cece-kuce.
https://www.tiktok.com/@kb_international/video/7586025966321929490?_t=ZS-92P0xQnV0pU&_r=1
Matar tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Hajiya A'Isha Buhari ta bayyana cutar da tawa tsohon shugaban Katutu har ya rasu.
Ta bayyana cewa, Shugaba Buhari yana fama da matsalar ciwon Sanyi.
Tace kuma ciwon ya samo asali ne daga aikinsa na soja lokacin yana matashi, suna shiga daji, kaya na bushewa a jikinsa bayan sun jike.
Sannan da sanyin AC, watau na'urar sanyaya daki ga kuma tsufa duk sun tarar masa a jiki.
Hakanan ta kawo cewa, Tsohon shugaban ya sha taba lokacin yana matashi wanda hakan ma ya taimaka wajan rashin lafiyar tasa.
Hajiya A'isha Buhari dai ta yi maganganu da yawa akan Marigayi Shugaba Buhari da suka baiwa mutane mamaki, wasu na ganin cewa bai kamata ta yi su ba.
Wani Barawon waya da ya shiga hannu ya koma yiwa mutane wa'azi.
Barawon yawa abokinsa da ya bashi waje ya zauna a gidansa satar wayane.
Saidai an jishi yana cewa Allah fa yace ku yafe idan an saba muku.
Kalli Bidiyon matashin anan
Wata matar aure me ciki ta dauki hankula bayan data nemi mijinta ya je makwabta ya roko mata shinkafa da fa duka da suka dafa.
An ga matar rike da kwano a wani Bidiyo da ya watsu sosai inda tacewa mijin nata ya shiga Makwabta ya roko mata shinkafar saboda tana son ci.
Saidai mijin yaki, yace ta je da kanta ta roko da kanta.
Ya nuna Tuwon da ya dafa a gidan inda yace me yasa ba zata ci ba?
Lamarin dai ya jawo muhawara me zafi.
https://twitter.com/metronaija/status/2002362363098325136?t=VHnTN94rnQQJgXJ5ptEFDg&s=19
Sabuwar motar gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Radda ta dauki hankula a kafafen sada zumunta inda ake ta maganarta.
A yayin da ake ta hasashe akan farashin motar.
Sarkin Mota ya bayyana farashin motar na gaskiya.
Yace farashin motar Naira Miliyan 300 ne.
Kuma yace kyauta aka baiwa gwamnan Katsinan Motar ba saye yayi ba.
https://twitter.com/SarkinMota_AMF/status/2002559586709143977?t=EuDlE6Uuw47xhNxo6NUC3g&s=19
Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC ta gargadi mutane akan kada su sayi Taliyar Indomie Vegetable Flavour noodles.
Dalili kuwa shine an gano wani sinadari a cikinta da ka iya yiwa Lafiyar Mutane illa.
Kamfanin Taliyar, ya bayar da umarnin 'yan kasuwa da suka sayeta su mayar da ita zuwa wajansu.
Kamfanin dake yin taliyar, Rappel Conso of France ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Hukumar NAFDAC tace an gano sinadarin ne bayan kai taliyar dakin bincike.
Wani Bidiyo ya bayyana inda aka ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda yayi Subul da baka ya kira Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Marigayi a wajan taro.
Yana kokarin yin maganane a kan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Saidai yayi sauri ya gyara.
https://twitter.com/Pharmacio001/status/2002252205244481957?t=YzEM95qX7SBMpD-0AiQyrA&s=19
Wasu 'yan matan Kannywood sun fito sun yi tonon Silili inda suka ce an hanasu daukaka ne saboda an nemesu sun ki bayar da kansu.
Sun ce duk macen daka gani a fim ko tsohuwa ko yarinya saida aka nemeta.
Ke bayar da labarin tace kai ko mahaifiyartace kuka gani a film to sai da aka nemeta.
https://www.tiktok.com/@activistmalcolmx1992/video/7585999104480742712?_t=ZS-92OHpxYMZwP&_r=1
Attajirin Najeriya, Abdulsamad Rabiu BUA kenan a wannan Bidiyon inda aka ganshi yana tuka jirgin ruwa a yayin da yake shakatawa.
https://www.tiktok.com/@abdulsamadrabiu_asr/video/7585965966471810325?_t=ZS-92OGJBzMvmC&_r=1