Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, bai kamata mutane da suka kai shekaru 70 zuwa 80 ba su rika karya.
Ya bayyana hakane a matsayin martani ga maganar Atiku Abubakar ta cewa sun hada kai dan kwace mulki daga hannun APC a shekarar 2027.
Kwankwaso ya bayyana cewa wannan magana bai san da ita ba kuma jinta ya bata masa rai.
Yace wannan ne matsalar Najeriya.
ya kara da cewa, Jam'iyyar PDP ta mutu ne shiyasa take nema sai ta hada kai da wasu jam'iyyun kamin ta samu nasarar karbar Mulki.
Bankin First Bank ya kori manyan ma'aikatansa su 100.
An kori ma'aikatanne dga aiki saboda su bada guri a nada sabbin jini su shugabanci harkar bankin.
Hakan na zuwane bayan da babban dan kasuwa, Femi Otedola ya sayi hannun jari mafi yawa a bankin wanda ya koma karkashin kulawarsa.
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja sun bayyana cewa, An kama wani mutum da muggan makamai a birnin tarayyar.
Mutumin me suna, Obinna Nwigwe An kamashi ne bayan samun bayanan sirri daga Najob Guest House dake Bwari.
A yayin da jami'an tsaro suka je kamashi, an iskeshi ya harbi wani mutum bayan da suka yi gaddama.
Bincike da aka yi sosai a gidansa an gano karin makamai da Albarusai.
wanda ya harba din, Andrew Philemonna can Asibiti yana jinya, a yayin da shi kuma ake bincike akansa.
Ana zargin wani matashi da kashe mahaifiyarsa sannan ya jefa gawarta a cikin rijiya a Jihar Cross River.
Lamarin ya farune ranar Lahadi a titin Chairman Road, dake garin Ohong karashin karamar hukumar Obudu na jihar.
A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook, an ga yanda mutanen unguwa suka taru ake zaro gawar matar daga rijiyar da dan nata ya jefata.
Rahotanni sunce wani abokinsa ne ya taimaka masa wajan gudanar da wannan danyen aikin.
Ya yiwa 'yar aikin gidansu baranar cewa idan ta sake ta gayawa wani sai ya kasheta.
Ya dauki yarinyar aikin gidan nasu akan mashin zuwa wani wajene inda akan hanya 'yan Bijilante suka taresu, anan ne Asirinsa ya tonu.
Babban fasto, Primate Ayodele ya bayyana abubuwan da zasu faru a shekarar 2025 kamar yanda ya saba yi duk shekara inda yake ikirarin an masa wahayi.
Faston yace wasu daga cikin abubuwan da aka masa wahayi shine cewa za'a saki shugaban kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra watau, Nnamdi Kanu, sannan matsin rayuwa zai karu a shekarar ta 2025.
Yace ya kuma gano cewa wani gwamna zai mutu, sannan za'a yi yunkurin kashe wani shugaban kasa ta hanyar zuba masa guba amma zai tsallake, saidai be bayyana kowane shugaban kasa bane.
Ya kuma za'a samu matsalar kisan jami'an tsaro na FBI da CIA na kasar Amurka.
Bayan Amarya Ta Gudu A Safiyar Ranar Daurin Aurensu, A Karshe Ango Ya Auri Daya Daga Cikin Kawayen Amarya A Ranar Auren
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne a garin Sabo-Ibadan dake jihar Oyo.
Me za ku ce?
A Yanzu Haka Za A Iya Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Sadaki, Inji Limamin Masallacin Albabello Dake Zaria
Malamin ya ce "kamar yadda ya tabbata a mazhabar Imam Malik za a iya biyan rub'u dinar ko darhami uku, inda dubu talatin ce kiyasin darhami uku", Inji- Imam Dr. Hamza Assudaniy Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Albabello Zaria.
Da Mu Da Kwankwaso Duk Tinubu Muka Yi Wa Aiki A Zaben 2023, Kuma Idan Har Kwankwason Da Na Sani Ne Zai Sake Sabunta Wannan Kwangilar A 2027, Inji Dan Bilki Kwamanda
Me za ku ce?