Wednesday, March 11
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon: Mawakiyar Najeriya, Teni ta kwanta Rashin Lafiya saboda an cire Najeriya daga gasar AFCON

Kalli Bidiyon: Mawakiyar Najeriya, Teni ta kwanta Rashin Lafiya saboda an cire Najeriya daga gasar AFCON

Duk Labarai
Tauraruwar mawakiyar Najeriya, Teni kenan inda ta kwanta rashin lafiya saboda an cire Najeriya daga gasar AFCON. Ta yi Bidiyo inda take gayawa 'yan kasar Ghana cewa sin ga abinda dan uwansu ya haddasa koh. Ta yi kira ga Shugaba Tinubu ya tura jirgin yaki zuwa kasar Ghana. https://twitter.com/i/status/2011708327647182982 Rafalin da ya hura wasan Najeriya da Morocco dai dan kasar Ghanane.
Kalli Bidiyon: Yanda Rikici ya bàrkè tsakanin wasu ‘yan Najeriya da ‘yan kasar Morocco bayan da aka yi yunkurin canja musu wajan zama a filin wasan da aka buga wasan jiya

Kalli Bidiyon: Yanda Rikici ya bàrkè tsakanin wasu ‘yan Najeriya da ‘yan kasar Morocco bayan da aka yi yunkurin canja musu wajan zama a filin wasan da aka buga wasan jiya

Duk Labarai
Wasu 'yan Najeriya da suka je kallon wasa a kasar Morocco sun yi rikici da hukumomin dake kula da filin wasan da aka buga jiya tsakanin Najeriya da Morocco. Sun shiga filin da wuri inda suka samu wuri suka zauna amma sai masu kula da filin wasan suka ce su tashi daga wajan su canja wajan zama. Saidai sun ce ba zasu tashi ba inda suka dauki abin suka watsa a Duniya. Sun yi zargin ana son a nuna musu banbanci ne da kaisu inda ba zasu iya baiwa Najeriya goyon bayan da ya kamata ba. A karshe dai masu kula da Stadium din sun kyalesu. https://twitter.com/i/status/2011494097614487592