‘Yan Najeriya na cikin wahala a matsin rayuwa, Rabon kayan abinci ba shine magani ba>>Inji Tsohon Kakakin Majalisar Dattijai, Ahmad Lawal
Tsohon kakakin majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya bayyana cewa, mutane na cikin matsin rayuwa kuma rabon kayan abinci ba shi bane mafita.
Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta bakin kakakinsa, Ezrel Tabiowo bayan da ya je mazabarsa dake jihar Yobe ya raba kayan tallafi.
Yace kamata yayi a samarwa mutane hanya da zasu dogara da kansu amma rabon abinci zai kawo sauki ne kawai na dan lokaci wanda kuma wahalar zata ci gaba.
Saidai yace kamin su kai ga wancan matsayi, su dake da halin bayarwa zasu ci gaba da bada tallafin dan saukakawa mutane rayuwa.
Yayi kira ga masu rike da madafan iko dasu dauki matakan da zasu kawowa Al'umma saukin rayuwa.