Thursday, September 17
Shadow
Kalli Bidiyon: Sunana Abdullahi Salihu, Kirista da danka ya koma sakamakon zagin da kakewa Malaman Sunnah irin su Sheikh Sani Yahya Jingir ne

Kalli Bidiyon: Sunana Abdullahi Salihu, Kirista da danka ya koma sakamakon zagin da kakewa Malaman Sunnah irin su Sheikh Sani Yahya Jingir ne

Duk Labarai
Wani Tsoho dan Jos ya fito inda yake ikirarin cewa tare suka yi yarinta da Sheikh Nura Khalid, Digital Imam. A cewarsa, yasan lokacin da idan Malam idan ya shawo giya yake faduwa a kofar gidansu har mahaifiyarsa ta fito da itace. A cewarsa sune suke kwace iccen da mahaifiyarsa ke daukowa. Yace sunansa Abdullahi Salihu kuma iftila'in da ya fadawa Sheikh Nura Khalid na komawar dansa Kirista, Sakamakon zagin da yakewa malaman Sunnah ne irin su Sheikh Sani Yahya Jingir. Yace kuma bala'i na Duniya ya ganshi saura na Lahira. https://www.tiktok.com/@baban.amira.baban5/video/7682401702443552021?_r=1&_t=ZS-99XWelnzr41
Bidiyon Dan Bello ya bankado aikin Amaja da ake yi na Titin Lagos zuwa Calabar

Bidiyon Dan Bello ya bankado aikin Amaja da ake yi na Titin Lagos zuwa Calabar

Duk Labarai
Wani Bidiyo da Dan Bello yayi ya dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan da ya bankado badakalar aikin Titin Legos zuwa Calabar. Dan Bello yace shekaru 2 ana aikin titin amma har yanzu bai wuce Kilometre 50 ba, har yanzu ba'a ma fita daga lagos ba. Sannan yace Titin yanzu haka har ya fara lalacewa sannan ya toshe hanyar wucewar ruwa wanda hakan ya kawo ambaliyar ruwa Yace wajan Bayar da kwangilar Titin ma son rai aka yi aka baiwa wasu 'yan kasar Lebanon aikin maimakon yanda aka saba bisa al'ada kowane kamfani ya gabatar da bukatarsa a duba wanda yafi cancanta. https://twitter.com/_nonconformist1/status/2096905809288483123
Tsohon dan majalisar tarayya ya nemi EFCC ta dawo da tsohuwar binciken da takewa Atiku Abubakar

Tsohon dan majalisar tarayya ya nemi EFCC ta dawo da tsohuwar binciken da takewa Atiku Abubakar

Duk Labarai
Tsohon dan majalisaf wakilai, Hon. Ehiozuwa J. Agbonayinma ya nemi EFCC ta dawo da binciken cin hanci da rashawa na shekarar 2006 da tawa Atiku Abubakar. Ya nemi cewa ya kamata a dawo da binciken kuma a hukunta Atiku Abubakar idan an sameshi da laifi. Saidai Jaridar Leadership ta nemi jin ta bakin hukumar EFCC amma wasu ma'aikatan hukumar da sukace suna son a sakaya sunayensu, sun ce hukumar ba zata binciki Atiku Abubakar ba musamman ganin yanda lamarin yayi kusa da zaben 2027. Atiku Abubakar yace wannan maganar banzace kamata yayi Gwamnati ta mayar da hankali wajan magance matsalolin 'yan Najeriya ba yi masa bita da kulli ba.
Wata Sabuwa Kalli Bidiyon: Ban ce na saki Matata Maryam Nicki Minaj ba, cewa na yi ta tafi gida>>Inji Gfresh Al-amin

Wata Sabuwa Kalli Bidiyon: Ban ce na saki Matata Maryam Nicki Minaj ba, cewa na yi ta tafi gida>>Inji Gfresh Al-amin

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, bai ce ya saki matarsa, Maryam Nicki Minaj ba. Yace ce mata yayi ta tafi gida kawai sai ganinta yayi a Kano. Ya kuma zargi Hassan Make-Up da cewa shine ya lalata masa aure inda yace tun tana cikin gidansa, Hassan na daga cikin masu hurewa Maryak Nicki Minaj kunne cewa idan ta fito zasu aureta. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7682541538500463880?_r=1&_t=ZS-99Wvhxu26Vh
Kalli Bidiyon: Wannan matashiyar inda take cewa duk masu cewa suna sonta tasan karza suke, kawai so suke ta basu kanta

Kalli Bidiyon: Wannan matashiyar inda take cewa duk masu cewa suna sonta tasan karza suke, kawai so suke ta basu kanta

Duk Labarai
Wannan matashiyar me suna Ama ta dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan kalamanta na cewa, duk masu cewa suna sonta kawai kaya suke son su ja. Tace su fito kawai su gaya mata gaskiya. Tace hakan ba matsala bane. Wannan kalamai nata sun jawo Allah wadai. https://www.tiktok.com/@ama2s222/video/7681993427810045204?_r=1&_t=ZS-99WtTEegwOj
Kalli Bidiyon: Wani da yayi shiga irin ta Ari Baba a gidan gala suke rawar Badala da wata yarinya akace Ari babane

Kalli Bidiyon: Wani da yayi shiga irin ta Ari Baba a gidan gala suke rawar Badala da wata yarinya akace Ari babane

Duk Labarai
Wannan wanine da yayi shiga irin ta Ari Baba a gidan gala suke rawar fitsara shi da wata matashiya ana cewa wai Ari Baba ne. Saidai da yawa sun bayyana cewa ba Ari Baba bane wani ne kawai yayi shiga irin tasa. Bidiyon ya jawo cece-kuce inda aka yi Allah wadai da lamarin. https://www.tiktok.com/@imranaibrahim820/video/7682392649034124564?_r=1&_t=ZS-99WrklnzEIv