Tuesday, July 7
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: Ji Sabon Sunan da Kwankwaso ya sakawa Abba

Kalli Bidiyon: Ji Sabon Sunan da Kwankwaso ya sakawa Abba

Duk Labarai
A yayin da siyasar Kano ta Dauki Dumi. Shugaban tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya fara mayar da martani a yayin da ake tsammanin gwamnab Kano, Abba Kabir Yusuf zai koma jam'iyyar APC. A wajan wani taro, Kwankwaso yace duk wanda ya bar tafiyarsu ta Kwankwasiyya, sunan siyasarsa 'yar Wada. https://twitter.com/i/status/2009515958189080598 Kwankwaso a baya dai ya bayyana cewa, Kamata yayi Abha ya ajiye musu kujerarsu kamin ya koma APC.
Kasar Amurka ta bayyana cewa a yanzu ta Fahimci ba Kiristoci kadai ake Mhuzghunawa a Najeriya ba

Kasar Amurka ta bayyana cewa a yanzu ta Fahimci ba Kiristoci kadai ake Mhuzghunawa a Najeriya ba

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, kasar ta ce ta fahimci hadda Musulmai ayyukan Tshàgyèràn Dhàjì na tabawa ba Kiristoci kadai bane. Hakanan shugaban kasar Donald Trump ya bayyana cewa idan ba'a daina Khisan ba, zai iya sake kawo Khari Najeriya. A baya dai, kasar Amurka ta kawo Khari Najeriya a jihar Sokoto. A yanzu dai ana ta tsammanin wace jiha ce kasar ta Amurka zata kawowa Khari? Wasu dai na cewa Jihar Borno.
Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 7 dan inganta Wutar Sola dake fadar shugaban kasa, watau Villa

Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 7 dan inganta Wutar Sola dake fadar shugaban kasa, watau Villa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan 7 dan inganta wutar Sola dake fadar shugaban kasar. An ware wadannan kudade ne a kasafin kudin shekarar 2026. A shekarar 2025 gwamnatin ta ware naira Biliyan 10 ne dan saka wutar Solar a fadar shugaban kasar. Hakan na zuwane a yayin da lamarin wutar lantarki ke kara tabarbarewa a Najeriya.
Kalli Bidiyon: Abinda wani Kirista yawa Sarkin Musulmi da ya sa ake ta masa Tofin Allah Tsynè

Kalli Bidiyon: Abinda wani Kirista yawa Sarkin Musulmi da ya sa ake ta masa Tofin Allah Tsynè

Duk Labarai
Wani Kirista ya wallafa Bidiyon me Alfarma Sarkin Musulmi da ya kirkira da AI wanda yake nuna cewa shi Kirista ne. Bidiyon ya jawo cece-kuce da Allah wadai sosai inda mutane ke ta kiran ya kamata a kamashi. Kiristan na zaunene a kasar Italiya, wasu sun ce sun aikawa hukumomin kasar Italiya da korafi akansa dan a hukuntashi. https://twitter.com/i/status/2009330648725717266 https://twitter.com/i/status/2009334310743236648